Zamfara: Wani babban dan siyasa ya fadi ya mutu haka kurin a wajen Biki

Zamfara tayi rashin babban me rike da mukumi muhimmi a jihar me wakiltar dukka daukacin kananan hukumomin dake har da Gusau.

Advertisements
Advertisements

Allah ya yi wa Dakta Malami Aliyu Yandoto rasuwa a ranar Asabar, a taron bikin diyar Yarima.

Yandoto shine shugaban hukumar kananan hukumomi ta jihar Zamfara kuma ya rasu bayan yanke jiki da yayi ya fadi.

Yandoto ya taba yin kwamishinan aikin noma sannan ya yi shugaban INEC na jihar Zamfara kafin rasuwarsa 

Shugaban hukumar kananan hukumomi ta jihar Zamfara, Dakta Malami Aliyu Yandoto mai shekaru 57 a duniya ya yanke jiki ya fadi, tare da mutuwa a wurin bikin diyar Sanata Ahmed Sani Yerima da dan Sanata Adamu Aliero. 

An yi daurin auren a gidan Yarima da ke Sokoto a ranar Asabar, 7 ga watan Nuwamban 2020 kuma ya samu halartar manyan ‘yan siyasa, jiga-jigai da kuma kusoshin gwamnati da suka hada da shugaban majalisar dattawan Najeriya. 

An gano cewa, bayan daurin auren, bakin da suka samu halarta sun garzaya gidan gwamnatin jihar Sokoto domin liyafar cin abincin rana. 

Bayan isar mamacin tare da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matwalle da wasu baki gidan gwamnatin, ya yanke jiki ya fadi inda yace ga garinku. 

Da gaggawa aka hanzarta kai shi asibiti a Sokoto inda aka tabbatar da mutuwarsa, shafin Linda Ikeji ya wallafa. 

Yandoto ya taba shugabancin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Zamfara inda daga bisani yayi kwamishinan aikin noma na jihar Zamfara. 

Gwamna Bello Matawalle ya nada shi shugaban hukumar kananan hukumomi na jihar, mukamin da ya rasu a kai kenan. 

An birnesa kamar yadda addinin Islama ya tanada a ranar Lahadi da safe a garin da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara. 

Babban mai mukami a Zamfara ya fadi ya mutu a wurin bikin diyar Sanata Yarima.

  Yan sanda sun tabbatar da sace yan Kasar China guda Biyu