‘Yan Ta’adda Sun Yiwa Mafarauci Yankan Rago

‘Yan ta’adda sun yi wa mafarauci yankan rago a Chiji da ke Abaji, cikin birnin Abuja a yayin da ya fita farauta.

Advertisements
Advertisements

Wani dan uwan mamacin ya bayyana cewa wuka suka yan danuwansa da shi kuma babu alamar harsashi.

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta ce tana bincike akan lamarin da nufin gano bata garin.

Wasu mahara sun yanka wani mafarauci mai shekara 47, Mista Wabari Ukpaka, a yankin Chiji da ke unguwar Abaji a birin Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin yankin, wanda ya bukaci a sakaya sunan shi ya ce lamarin ya faru ranar Alhamis din da ta wuce, bayan marigayin ya bar gida da misalin 4:00 na yamma don zuwa farauta a dajin da ke yankin.

  Birgediya M. Yerima: An kori kare anbar tunk|Munanan halayensa a zayyane|

Gwamna Bagudu Ya ce mamacin ya yi fakin din babur dinsa a gonarsa kuma ya shiga jeji don farutar nama da bindigarsa irin ta mafarauta amma wasu mahara suka kama shi kuma suka yi masa yankan rago.

Iyalansa sunyi ta tsammanin dawowar sa da naman da ya farauto wanda za su yi bikin kirismeti, har zuwa yammacin juma’a, lokacin da aka gano yasasshiyar gawar sa da makwogwaran sa a yanke a cewar sa.

Daya daga cikin iyalan mamacin ya shaida wa wakilinmu cewa babu alamar harsashi a jikin sa ya kuma kara da cewa maharan sunyi amfani da wuka mai kaifi wajen yanka wuyansa.

  Najeriya @ 60: Yahaya Kwande ya fadi kausasan maganganu akan Najeriya

A takaice, babu alamar ciwon harsashi a jikin sa lokacin da muka je neman sa.

Mun gano gawar sa an yanka makwogwaransa kuma an yar da gawar sa inda mutane zasu ganta cikin sauki, a cewar sa.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf, ta ce hukumar ta na bincike akan lamarin.

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam’iyyar ta mutu.

  Ankama wasu mutane suna cin babbakakken naman "yan sanda

A wurin gasar gano zakarun ‘yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.