Yan taadda sun kashe mutum 7 a kasuwa, sun kona tirela daya

Mutum 7 ne suka rasa rayukansu wadanda suka hada da ‘yan sa kai 2 a Galadimawa

Advertisements
Advertisements

Miyagun ‘yan bindiga sun kai hari kasuwar mako ta Galadimawa da ke Giwa jihar Kaduna

Babu kakkautawa jami’an tsaro suka bi su inda suka ragargaza wasu yayin da wasu suka tsere

A kalla mutum bakwai da suka hada da ‘yan sa kai biyu suka mutu bayan ‘yan bindiga sun bude musu wuta a kasuwar mako ta Galadimawa da ke karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Kamar yadda Samuel Aruwan, kwamishinan cikin gida ya sanar a ranar Alhamis, ‘yan ta’addan sun shiga kasuwar wurin karfe 4 na yammacin ranar Laraba kuma suka bude wa jama’a wuta.

  President of Nigeria Republic Discloses Why All the Citizens Should Take Covid 19 Vaccine

Aruwan ya bada sunayen wadanda aka kashe kamar haka:

Yusuf Magaji Iyatawa, Dabo Bafillace, Danjuma Haladu, Shuaibu Isyaku, Isyaku Adamu, Shehu Dalhatu da Musa Haruna Kerawa

Ya kara da cewa wani direba mai suna Yusuf Tumburku wanda ya gama yin lodi ya fuskanci ibtila’i domin kuwa miyagun sun banka wa motar wuta.

Akwai wata mota da miyagun suka banka wa wuta, Aruwan yace.

Kwamishinan ya kara da bayyana cewa hukumomin tsaro da suka hada da ‘yan sanda tare da sojoji sun banki miyagun inda suka tsere.

Ya ce ‘yan bindiga da suka isa wurin suna kan babura a kalla 15 kuma jami’an tsaron sun yi nasarar halaka wasu daga ciki

  Yanzunnan Fada ya Barke Tsakanin Hausawa da Yarbawa a Lagas

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya mika ta’aziyyarsa ga iayalan wadanda suka rasa rayukansu.