Yan sanda sun tabbatar da sace yan Kasar China guda Biyu

Yan sanda a jihar Osun ta tabbatar da sace wasu yan ƙasar China mazauna Najeriya guda biyu a ranar litinin 5 ga watan Afrilu.

Advertisements
Advertisements

Yan sandan sun ce an sace mutanen biyu ne a wurin haƙar ma’adanan ƙasa dake ƙauyen Okepa/Itikan dake jihar ta Osun

Kwamishinan yan sandan jihar ya haɗa jami’an tsaron haɗin guiwa don ganin an ceto mutanen an kuma kamo yan bindigar

Rundunar yan sanda reshen jihar Osun sun tabbatar da sace wasu yan ƙasar China mazauna Najeriya a ranar Talata, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Hukumar ta bayyana cewa yan bindigar sun sace Zhao Juan, dan shekara 33 da kuma One Wen, ɗan kimanin shekara 50 a wajen haƙar ma’adanai na jihar.

  Gomnati ta sake bada sabon tsari game da Karin kudin Wutar Lantarki

An sace mutanen biyu a wajen haƙar ma’adanai dake ƙauyen Okepa/Itikan ƙaramar hukumar Atakumosa ta yamma a jihar Osun a ranar Litinin 5 ga watan Afrilu.

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigar sun kai hari wurin ne da yawan su, suka fara musayar wuta da jami’an tsaron wurin na tsawon awa ɗaya kafin daga bisani su ci ƙarfin jami’an tsaron.

A jawabin da mai magana da yawun yan sandan jihar, Yemisi Opalola ya yi, ya ce yan bindigar sun harbe jami’an tsaro masu zaman kansu guda biyu kafin daga bisani su yi awon gaba da mutanen.

Daga faruwar lamarin ne, kwamishinan yan sandan jihar, CP Olawale Olokode, ya tura jami’an tsaro cikin gaggawa zuwa wurin da abun ya faru.

  Amarya ta mutu a ranar aurenta a karamar hukumar Funtua-Katsina

Kwamishinan ya tura jami’an tsaro da suka haɗa da, yan sanda, jami’an sa kai na JTF, da sauran jami’an tsaro waɗanda suka shiga neman yan bindigar don kuɓutar da waɗanda aka sace da kuma kama waɗanda suka yi wannan aika-aika.