Yan sanda sun sami nasarar Kashe Bobrizky babban dan bindiga

Bayan kisan Terwase Gana a Benue, an sake samun nasarar kashe wani shahrarren dan bindiga

Advertisements
Advertisements

Jami’an yan sanda sun bindiga Bobisky ne a jiharsa ta Rivers

Gabanin kisansa, gwamnati tana nemansa ruwa a jallo

Wani kasurgumin dan fashi kuma mai garkuwa da mutane da ya addabi jihar Rivers, Honest Digbara wanda aka fi sani da Bobisky, ya gamu da ajalinsa hannun jami’an hukumar yan sanda.

An bindige dan bindigan wanda aka dade ana nema ruwa a jallo ne ranar Asabar.

Related Post

Al’ummar jihar sun shiga murna da farin ciki yayinda suka samu labarin mutuwan Bobisky.

Gabanin samun nasarar hallakashi, gwamnati ta yi alkawarin kudi milyan 30 ga duk wanda ya ke da labarin inda dan bindiga yake.

An damke shine a wani harin bazata da hukumar yan sandan Rivers ta kai garin Korokoro dake karamar hukumar Tai ta jihar.

Bobisky ya dade yana ta’asa a sassan jihar kafin gamuwa da ajalinsa.