Yan boko Haram sunyiwa sojojin Najeriya gadar zare a safiyar yau

Yan Boko Haram sun shiryawa dakarun rundunar soji a kauyen Doska da ke karamar hukumar Damboa a jihar Borno

Advertisements
Advertisements

Majiyar soji ta sanar da TheCable cewa an kashe sojoji bakwai tare da raunata wasu goma sha kwai

Mayakan kungiyar Boko Haram da ke kauyen Doska da kewaye sun yi kaurin suna wajen kadaddamar da harin kwanton bauna a kan dakarun soji

A kalla dakarun rundunar soji bakwai ne suka rasa ransu bayan mayakan kungiyar Boko Haram sun shirya musu gadar zare a Doska, jihar Borno, kamar yadda jaridar TheCable ta wallafa cewa majiyar soji ta tabbatar mata.

TheCable ta rawaito cewa dakarun rundunar soji sun fita faturu ne zuwa yankin Doska a yayin da suka ci karo da mayakan kungiyar Boko Haram sanye da kakin soji da kuma motoci masu dauke da bindigu.

  Spanish LaLiga News: Barcelona raise prodigy Ansu Fati's phrase.

Doska wani kauye ne a tsakanin garin Ajigin da Talata a karamar hukumar Damboa a jihar Borno da jama’a suka kauracewa tun shekarar 2015 bayan mayakan kungiyar Boko Haram sun kwace iko da kauyen.

Har yanzu kauyen Doska na daga cikin wuraren da mayakan kungiyar Boko Haram keda karfi.

“Dakarun rundunar sojin sun fita faturu ne zuwa Doska lokacin da suka hadu da mutane a cikin kakin soji da motoci da makaman sojoji, sun ma dagawa sojoji hannu a zuwan sojoji ne daga wani sansanin.”

“Rundunar sojojinmu ta tsaya tare da gaisawa da wadannan mutane bisa tunanin sojoji ne.

Suna yin gaba daga wurin aka kai musu harin kwanton bauna, sai wadancan mayakan suka juyo, suka tarfa sojojinmu, suka bude musu muta ta kowanne bangare.

  Lionel Messi vows to quit Barcelona if the club does not meet his demands

“Mun rasa sojoji bakwai, guda 17 sun samu munanan raunuka,” a cewar majiyar.

Mayakan Boko Haram da ke yankin Doska da kewaye sun yi kaurin suna wajen kaddamar da harin kwanton bauna a kan rundunar soji tare da yin awon gaba da makamansu da sauran kayansu.

Yunkurin jin ta bakin kakakin rundunar soji, Kanal Sagir Musa, a kan lamarin bai samu ba ya zuwa lokacin wallafa rahoto