Yan Boko Haram sunyi shirin kai Hari a birnin tarayya

Gwamnatin Najeriya ta bayyanawa cewa yan ta’addan Boko Haram na shirin kai farmaki babbar birnin tarayya Abuja, da jihohin da ke makwabtaka da su.

Advertisements
Advertisements
yan boko haram sun bayar da takardar sanarwa akan harin da suke son kaiwa Abuja da sauran yankunan dake gefen na birnin tarayyar

Gwamnatin ta ce yan ta’addan na shirin kai hari ne wasu wurare na musamman a birnin tarayya kuma tuni sun kafa mabuya guda biyar a Abuja.

A cewar wata takardar da Kontrollan hukumar hana fasa kwabri wato kwastam, H.A Sabo, ya saki ranar 20 ga Agusta, 2020, ya bukaci dukkan hafsoshin su kasance cikin farga, Sahara Reporter ta ruwaito.

Boko Haram na shirin kai gari Abuja, Kogi da Nasarawa - Gwamnatin tarayya
Boko Haram na shirin kai gari Abuja, Kogi da Nasarawa – Gwamnatin tarayya

Takardar tace: “Labarin da Kontrola Janar na hukumar Kwasta ya samu ya nuna cewa akwai mabuyan yan ta’addan Boko Haram a ciki da wajen birnin tarayya Abuja.”

“Karin bayani ya nuna cewa suna shirin kai hari wasu wurare cikin birnin.”

“An samu rahoton cewa sun kasa sansani a wuraren nan; Dajin Kunyam, hanyar tasahar jirgin sama Abuja, Dajin Rubochi/Gwagwalada, Dajin Kuje Abuja, Dajin Unaisha a karamar hukumar Toto na jihar Nasarawa, Gegu, kusa da garin Idu a jihar Kogi.”

“Saboda haka, ana sanar da ku kasance cikin tsaro a koda yaushe. Ku tabbatar labarin nan ya yadu.

Za ku tuna cewa harin farko da aka taba kaiwa Abuja ranar 1 ga Oktoba, 2010, yan watanni bayan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

  2,200 People recruited for school feeding program in Kogi