‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Hudu a Kaduna

‘Yan bindiga sun kashe mutane 4 tare da yin garkuwa da mata a kauyen Katarma a Jihar Kaduna. 

Advertisements
Advertisements

Kwamishinan tsaro, Aruwan ya ce an ceto gaba daya matan da aka yi garkuwa da su. 

Yan bindiga

Akwai jami’an sintiri daga cikin mutanen da yan bindigar suka kashe. 

‘Yan bindiga sun kai hari ranar Laraba kauyen Katarma a karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna, tare da kashe mutum hudu ciki harda jami’an sintiri kafin su yi garkuwa da wasu mata a yankin. 

A rahoton jami’an tsaro, jami’an sintiri ne suka fara suka fara tunkarar yan bindigar kafin daga bisani jami’an tsaro su shiga kauyen.

Mutane hudun da lamarin sune Bulus Barde, Hassan Zarmai, Lawal Pada da kuma Kefas Auta wanda aka kashe a musayar wuta.

Sauran mutum uku, Amos Doma, Zamba Ali da Bomboi Busa sun samu raunika a musayar wutar.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa, ya ce an ceto gaba daya matan da aka sace.

A cewar sa, da ake mayar da martanin harin, an tura rundunar sojojin sama kauyen Katarma da Kusasu da ke jihar Niger.

Su kuma sojojin kasa suka ci gaba da bibiyar su yayin sojojin sama suka kashe yan bindiga da dama.

Aruwan ya ce an hangi yan bindiga a Katarma, wanda suka tara garken shanu suna kokarin guduwa akan babura.

Jami’an sojin sama sun kashe su ta jirgi. 

  Yanzu Yanzu: Sojojin Najeriy sun kashe kwamandojin Boko Haram 7 a Chadi