Yan bindiga: Gaskiyar magana akan dawowar yanda aka sace a GSS Kankara

Yan bindiga sun samu damar yin awon gaba da kimanin dalibai 400 a makarantar sakandaren gobnati dake karamar hukumar Kankara dake jiihar Katsina.

Yan bindiga sun samu damar yin awon gaba da kimanin dalibai 400 a makarantar sakandaren gobnati dake karamar hukumar Kankara dake jiihar Katsina.

Advertisements
Advertisements

Bayan sace yaran iyaye da malamai babu wanda hankalinsa ya kwanta kullin cikin nemansu ake.

A daren da aka sace yaran shugaba muhammad Buhari ya zo mahaifarsa wato garin Daura wanda wasu daga cikin mutanen dake zaune a Unguwar su ya bayyana.

Daga kafafen watsa labarai ana jita jitar cewa shuagaban kasan yaje ya jajantawa jamaar da abin ya shafa.

Jaridar Legit ta ruwaito daga jaridar The Nation cewa yaran da aka kama sun dawo tareda raunuka jikin su sakamakon gudun da suka dinga yi a daji kuma da daddare.

A wasu kafafen kuwa an karyata wannan batu na dawowarsu kamar inda Fugitive News ta samu zantawa da wani dake cikin bangaren na malaman makarantar cewa “Dalibai 600 garemu yanzu saura 200 kadai

Related Post

Bayanansa na nuni da cewa dalibai 600 garesu amma an sace 200 wanda haryanzu basu dawo ba.

Ya kara da cewa haryanzu ba su dawo ba amma ansan dajin da aka shiga dasu suma nan a dajin kankara.

Rahoto ya nuna cewa gomnatin jihar Katsina taki bada umarni a shiga dajin ayi bata kashi saboda gudun kada a rasa rayuka da yawa na wadanda basujiba ba su gani ba.

Amma har yanzu matakan tsaro na nan a wajen ana tina nin yanda zaa kubuta dasu duka ba tare da wani ya salwanta ba a cikinsu.