Yajin aiki: Ministan kwadago ya baiyana ranar da ASSU zata janye yajin aiki

Ministan kwadago, Dr Chris Ngige ya bayyana cewa ma’aikatun kudi, ilimi, kwadago da ofishin babban akawun kasar za su gana da kungiyar malaman ASUU

Advertisements
Advertisements

Hakan na daga cikin yunkurin da suke na neman maslaha da janye yajin aiki da malaman suka tafi

Ngige ya kuma bayar da tabbacin cewa kwanan nan kungiyar ta ASUU za ta janye jakin aikin nata

Ministan kwadago da daukar ma’aikata, Dr Chris Ngige, a yammacin ranar Talata, ya bayyana cewa ma’aikatun kudi, ilimi, kwadago da ofishin babban akawun kasar za su gana da kungiyar malaman jami’a (ASUU).

Ngige ya ce za su gana ne domin magance matsalolin da ke damun fannin ilimi.

  Gwamnatin jihar katsina ta ceto kimanin mutane 103 a hannun miyagu

Da yake bayyana hakan a lokacin da ya bayyana a wani shirin Channels Television, tsohon gwamnan na Anambra ya bayyana cewa ASUU za ta janye yajin aiki kwanan nan.

Ya ce: “Kwanan nan lamarin ASUU zai zo karshe.

Dalilai biyu- ASUU ta kira gwamnatin tarayya, bisa wakilcin ma’aikatar kudi da ofishin babban akawu da ma’aikatansu, ma’aikatar ilimi domin su zo don gwaji.

“Mun shirya aikata hakan. Bayan bikin yancin kai, ma’aikatu hudu da hukumomin da abun ya shafa za su hadu da ASUU. Za mu duba tsarin UTAS.

Ko akwai matsala tattare da IPPIS kamar yadda tayi korafi wanda UTAS ta gyara. Menene aibu a game dashi? Manhaja ne, za mu yi duba zuwa gare shi.

“Abu na biyu, mambobin kungiyar ASUU na ta karban kudadensu tun da annobar COVID-19 ta billo kuma na rubuta wata takarda zuwa ga Shugaban kasa cewa mambobin ASUU yan Najeriya ne har yanzu.

Hatta mambobin, suna da iyali da suka daukar dawainiyarsu. Zuwa mako na sama, za mu yi tanadi ga wannan zanga-zanga.”

A baya Legit.ng ta kawo cewa, kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU a ranar Talata ta sanarwa gwamnatin tarayya cewa ta zabi amfani da tsarin ‘University Transparency and Accountability Solution’ wajen biyan albashi.

  Buhari: Aikin banza Shuka dusa a ruwa-Taaziya

Kungiyar ta ce ta zabi tsarin UTAS ne domin ya zama kishiyar tsarin da gwamnatin ta gabatar na IPPIS, tana mai nuni da cewa sabon tsarin zai fi dacewa da su.

A cewar ASUU, manhajar UTAS an kammalata kuma an gabatar da ita ga ma’aikatar Ilimi da sashen manyan ma’aikata na ma’aiktar.