Wata ta Rabu da Saurayinta ta Sanadiyyar Kin Fara Yahoo

Wata ta rabu da saurayinta saboda ta umarceshi daya fara yahoo shikuma ya bijire.

Advertisements
Advertisements

Kamar yadda ya walllafa, ta so ya zama dan damfarar yanar gizo don har na’ura mai kwakwalwa ta siya mishi kyauta

– Ta sanar da shi cewa bata farin ciki da albashinsa don haka dole ya samo hanyar samo musu manyan kudade

Wani matashi dan Najeriya ya bar jama’a a kafar sada zumuntar zamani cike da mamaki bayan ya bada labarin rabuwarsa da tsohuwar budurwarsa.

Ya ce ta bashi na’ura mai kwakwalwa kyauta a ranar zagayowar haihuwarsa domin ya fara damfara a yanar gizo.

Kamar yadda ya bayyana a labarin, ta ce bata jin dadin albashinsa domin baya isarsu.

Don haka ta bashi kyautar ne don ya shiga gungun wasu masu damfarar yanar gizo.

Na tuna lokacin da muke soyayya da tsohuwar budurwata. Ta bani kyautar na’ura mai kwakwalwa. Na yi mamakin kyautar.

“Hakan yasa na tambayeta na menene.

A take ta sanar da ni cewa albashina ne baya isarta kuma tana so in fara damfarar yanar gizo. Na ce mata ba zan iya ba.

  Yanzunnan Fada ya Barke Tsakanin Hausawa da Yarbawa a Lagas

1 thought on “Wata ta Rabu da Saurayinta ta Sanadiyyar Kin Fara Yahoo