Wata budurwa ta chakawa saurayinta wuka

Wata budurwa ta cakawa saurayinta wuka ya mutu sakamakon ciki da yayi mata

Advertisements
Advertisements

Budurwar taki yarda a zubar da cikin bayan saurayin ya bukaci hakan, amma daga baya ta bukaci ya bata kudi yaki yarda

An gano wuka da jini a jikinta a inda lamarin ya faru, sannan kuma an gano inda ta caka masa wukar a kirji a asibiti

Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta kama wata budurwa mai shekaru 25, mai suna Oyinye Chime, wacce ke dauke da ciki, da laifin cakawa saurayinta mai suna Eleyi Azubuike wuka, inda hakan yayi sanadiyyar mutuwar shi a gidanshi dake Ochiagha dake Nkpor, a cikin jihar ranar Laraba 2 ga watan Satumba.

  Real Madrid is ready to give £70m offer to Guners striker Aubameyang

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Muhammed Haruna, wanda ya bayyana haka ga manema labarai, ya ce ‘yan sandan sun karbi rahoton kisan, suka kuma yi gaggawar kai ziyara wajen da lamarin ya faru a ranar Laraba din.

“Bincike ya nuna cewa marigayin ya yiwa budurwar ciki, sai ya bukaci a zubar da cikin, sai taki yadda, ita ma ta bukaci ya bata kudi da za ta kula da yaron, sai shima yaki yadda. Hakan yayi sanadiyyar rikici ya barke tsakanin masoyan har yayi sanadiyyar mutuwar marigayin.”

A cewar Haruna, ‘yan sanda dake aiki a ofishin dake Ogidi, tare da shugabancin DPO CSP Ekuri Remigius, sun kai ziyara wajen da lamarin ya faru inda suka yi gaggawar garzayawa da marigayin asibitin Enu Mission dake Ogidi domin ceto rayuwar shi, inda a asibitin ne aka tabbatar da cewa ya mutu.

  Spanish LaLiga News: Lionel Messi Confiscate hat-trick as FC Barcelona route Mallorca.

Ya ce bayan sun gabatar da bincike sun gano wurin da aka caka masa wuka a kirji, sannan kuma an gano wuka da jini a jikinta a gidan da lamarin ya faru.

Kakakin ya ce har yanzu suna kan bincike akan gano ainahin abinda ya jawo wannan lamari.

Kakakin ya ce har yanzu suna kan bincike akan gano ainahin abinda ya jawo wannan lamari.