Wasu yan bindiga sun bankawa ofishin yansanda wuta yanzu-yanzu

Wasu yan bindiga sun sake bankawa ofishin yan sanda wuta a jihar Imo, yan awanni bayan ziyarar da mataimakin shugaban kasa da Sifeto Janar na yan sanda, IGP Adamu suka kai ziyara jihar.

Advertisements
Advertisements

Tafiyar Osinbaji ke da wuya, yan bindigan suka banka wuta hedkwatar yans andan karamar hukumar Ehime Mbano.

The Nation ta tattaro cewa suna dira ofishin yan sandan suka kubutar da dukkan wadanda ke tsare sannan suka banka wuta.

Hakazalika an samu labarin cewa sun gudanar da hakan ba tare da wani ya yi yunkurin dakatad da su ba.

Wata majiya tace: “Yan bindiga da yamman nan sun kona hedkwatar yan sanda na karamar hukumar Ehime Mbano.

  Yan bindiga: Gaskiyar magana akan dawowar yanda aka sace a GSS Kankara

Daga isarsu, sun kubutar da wadanda ke tsare kafin aika-aikan da suka yi.”

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Orlando Ikeokwu, ya bayyana cewa bai samu labarin harin ba.

Amma wani babban jami’in dan sanda wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa hukumar bata ji dadin wannan sabon harin ba.