Wasu Daga Cikin Matasan Najeriya Masu karancin Shekaru da Miliyoyin Kudi

Wasu daga cikin matasan Najeriya da suka samu kudi nasu na kansu a kananan shekaru kuma za a iya kiransu miloniyoyi a 2021

Advertisements
Advertisements
  • Marubuciya kuma mai tarin dukiya Linda Ikeji za a iya saka ta cikin wannan jerin a matsayin kallabi tsakanin rawuna

Wadannan matasan masu kananan shekaru ‘yan kasuwa ne kuma suna da labarai masu tarin mamaki dangane da dukiyarsu

Ana cewa komai tabarbarewar tattalin arzikin kasa, dole ne a samu wadanda suka samu riba a wannan lokacin.

Kamar yadda Legit.ng ta tattaro, ga miloniyoyi biyar matasa na Najeriya da tauraruwarsu ke haskawa tare da labaran yadda suka tara dukiyoyinsu.

5. Jason Njoku

Matashin mai shekaru 39 ya zo a lamba ta 5. Dan kasuwa ne kuma shine wanda ya samo Spark, wani kasuwanci mai jarin $2 miliyan kamar yadda nigeriafinder.com ta tabbatar.

Mashiryin fina-finan ya kasance mai saka hannayen jari a manyan kasuwanci a Afrika. Tare da shi aka samar da iROKOtv.

4. Linda Ikeji

Marubuciya Linda Ifeoma Ikeji ita kadai ce mace da ta shigo wannan jerin inda ta zama a lamba ta hudu.

Macen mai shekaru 40 ta mallaki gidan talabijin mai suna Linda Ikeji TV.

Matar ta tamfatsa ginin gidanta mai kayatarwa a 2016 kuma an san ta da son kyale-kyale.

3. Igho Sanomi

Shine ya kafa Taleveras Group. Igho Sanomi da ne ga tsohon mataimakin sifeta janar na ‘yan sanda kuma shine ya zo a mataki na uku.

Matashin dan kasuwan yana samun miliyoyin naira daga fannin lantarki, gine-gine da sauransu.

An gano cewa kamfaninsa yana ba babban kaso a wasu rijiyoyin man fetur guda biyu.

2. Ladi Delano

Kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana, yana daga cikin wadanda ake hangowa a makomar kasuwancin kasar nan, Ladi Delano ya zo a lamba ta biyu a wannan jerin.

Ladi yana daga cikin manyan jiga-jigan da suka kafa Bakrie Delano Afrika mai darajar $1 biliyan.

Wannan kasuwancin ya mayar da hankali ne wurin hakar ma’adanai, aikin noma da kiwo da kuma bangaren man fetur da iskar gas.

1. Sijibomi Ogundele

Sijibomi Ogundele mai shekaru 36 matashi ne mai tarin dukiya.

Dan kasuwa ne da ya mayar da hankali wurin harkar dillanci, siyarwa tare da gina gidaje.

  Adebiyi Ya Sanar da Ranar Kammala Titin Abuja-Kaduna-Kano