Wani Gomna a Najeriya ya bukaci abayar da damar rike bindiga

Wani Governor a Nigeria ya bukaci abayar da damar rike bindiga

Gwamnan Binuwai Samuel Ortom ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta bai wa ’yan Najeriya izinin mallakar bindiga kirar AK47 don kare kansu daga mahara. 

Advertisements
Advertisements

Gwamna Ortom ya yi kiran ne yayin gabatar da wata takarda lokacin tattaunawarsa da cibiyar inganta shugabanci (CVL) tare da hadin gwiwar Kungiyar Gwamnonin Najeriya.

Taron ya bukaci a yi dokar da za ta bai wa ’yan kasa izinin mallakar makamai da kuma hukunta wadanda suke rike da su babu lasisi.

A takardar da ya gabatar mai taken, ’Kalubalen tsaro da matsalolin shugabanci a wannan lokaci”, Ortom ya bukaci dukkannin matakan gwamnati su fahimci cewa kalubalen tsaro yana yin cikas ga ci gaban kasa, don haka su tashi su magance ta.

Related Post

Ya kuma yi kira da a wadatar da hukumomin tsaro da kayan aiki tare da horar da jami’ansu don magance kalubalen tsaro.

Gwamnan ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da dokar samar da labin makiyaya don magance rikicin makiyaya da manoma.

“Akwai bukatar a wayar da kan jama’a musamman matasa don su zama ’yan kasa nagari”, inji shi.