UNICEF ta Chacchaki Ganduje akan Daure Mawakin Batanci a Kano

Majalisar Dinkin Duniya bangaren UNICEF ta yi Alla-wadai da hukuncin da kotun Kano ta yanke wa wani mai shekaru 13, Omar Faruk na shekaru 10 a gidan yari

Advertisements
Advertisements

Kotun shari’a ce ta yanke wa Farouq hukunccin bayan samunsa da laifin yin batanci ga addinin Islama

UNICEF ta ce hakan ya sabawa ‘yancin kare hakkokin yara kanana da kuma yi musu adalci wanda Najeriya ta rattaba hannu a kai a shekarar 1991

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ta yi watsi da hukuncin shekaru 10 a gidan yari da wata kotun shari’a da ke Kano ta yankewa matashi dan shekaru 13, Omar Farouq.

  Dahiru Usman Bauchi, ya musanta goyon bayan Mailafia a kan ikirarinsa

Kotun shari’ar Musulunci da ke Feli Hockey, jihar Kano ta yanke wa Farouq hukuncin ne bayan ta same shi da laifin yin batanci ga addinin Islama a ranar 10 ga watan Agusta.

Da take martani kan lamarin, kungiyar a cikin wani jawabi, a ranar Laraba, ta hannun wakilinta a Najeriya, Peter Hawkins, ta bayyana matakin a matsayin ba daidai ba.

UNICEF ta bayyana hakan a matsayin wanda ya sabawa ‘yancin kare hakkokin yara kanana da kuma yi musu adalci wanda Najeriya ta rattaba hannu a kai a shekarar 1991.

Jawabin ya ce: “Yankewa wannan yaro dan shekara 13 Omar Farouk hukuncin shekaru 10 a gidan yari da aiki mai wahala ba daidai bane,” in ji Peter Hawkins.

  KADPOLY: Wani lecturer ya harbe matarsa sannan ya kashe kansa

“Ya kuma sabawa yancin kare hakkokin yara kanana da kuma yi musu adalci wanda Najeriya da jihar Kano suka rattaba hannu.”

Ya kara da cewa: “hukuncin ya yi karo da sharadin Majalisar Dinkin Duniya kan yancin yara, wanda Najeriya ta rattaba haannu a kai a 1991.

Ya kuma saba ma dokar Afrika kan hakki da walwalan kananan yara wanda Najeriya ta rattaba hannu a 2001, da kuma dokar yancin yara na 2003.”

Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Kano da su gaggauta sake yin nazari kan hukuncin da aka yankewa matashin, jaridar Vanguard ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Zargin luwadi: Kotu ta bukaci a adana mata makaho a gidan yari

  Kisan Gilla: Hauwa'u ta zayyana Dalilinda yasa ta kashe 'ya'yan Cikinta

A gefe guda, babban lauyan Najeriya, Femi Falana, ya mika korafi ga hukumar kare hakkin dan Adam da ke Banjul, Gambia, a kan hukuncin kisa da aka yanke wa mawakin Kano.

Falana ya bukaci hukumar da ta yi amfani da karfin isarta kamar yadda dokokin hukumar ta bayyana na 2020.