Tsandareriyar budurwa na neman saurayi ta hanyar saka hotunanta a yanar gizo

A ranar juma’a, 25 ga watan Satumba, wata kyakkyawar budurwa ta garzaya shafin sada zumuntar zamani na Twitter tana neman saurayin da zai nuna mata soyayya

Advertisements
Advertisements

Wallafar budurwar ta kawo cece-kuce inda wasu suke cewa bazasu iya bin ta ba, wasu kuma sun nuna yabawa kwarai

A wallafar ta, @adethayorr ta gwada wa samari idan da wanda ke sonta, kada yayi kasa a guiwa ya sanar da ita cikin sauri

Wata kyakkyawar budurwa mai cikakken diri ta garzaya shafin sada zumuntar zamani na Twitter, in da take amfani da suna @adethayorr tana bawa samari dama.

A wallafar ta ta ranar Juma’a, 25 ga watan Satumba, ta sanar da samari cewa in dai akwai wanda ya ga ta burgeshi, to yayi magana.

  Makiyayin da yaso Auren Zahra Buhari kuma dagaske a ransa

Kamar yadda al’adar Afirika take, samari ne suke irin wannan abu da @adethayorr tayi. Hakan ya jawo surutai iri-iri akan wannan wallafar.

Dirarriyar budurwa ta wallafa hotunanta, ta bukaci duk saurayin da ke da bukata ya nemi soyayyarta. Hoto daga @adethayorr

Budurwar ta wallafa hotunanta guda biyu, tare da nuna duk mai bukatar soyayyar ta ya bayyana mata.

Ta dauki hoton da wani bakin tabarau da kuma bakaken kaya wadanda suka fitar da surarta kwarai.

Sai ta wallafa, “ka bayyanar da soyayyarka, ta yiwu in so ka!”

Wani @Bode4sure81gma1 ya ce, “A ina kike a Abuja? Zanso mu dan yawata tare”.

Wani @Ozikroh ya ce, “a’a a kai kasuwa.”

Haka samari sukayi ta maganganu, wasu suce baza su iya ba, wasu kuma suna cewa a gaskiya takai budurwar da za’a gani a fadi.

  Kisan Gilla: Hauwa'u ta zayyana Dalilinda yasa ta kashe 'ya'yan Cikinta

A wani labari na daban, wata ‘yar Najeriya mai suna Hauwa Ojeifo ta samu gagarumar kyauta ta musamman daga gidauniyar Bill Gates da Melinda Gates ta shekarar 2020.

Kasancewar budurwar mai rajin kare hakkin jinsi da nakasassu ce, tana jagorantar wata kungiya mai taimako da bada shawarwari ga masu fama da rashin lafiyar kwakwalwa.

Hauwa Ojeifo tana bawa masu damuwa karfin gwuiwa ne ta hanyar basu labarin rayuwarta da irin kalubalen da ta fuskanta.