Toh fa! Rigiji Gabji!!! Fada ya kaure tsakanin Gwamnan Bauch da na Ondo

Toh fa! , Gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Rotimi Akeredolu, ya caccaki gwamnan jihar Bauchi, Bala AbdulKadir, kuma ya siffanta shi matsayin mumunan dan rikici da tarzoma.

Advertisements
Advertisements

Akeredolu wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin yankin kudu maso yamma ya yi Bala Kauran wankin babban bargo ne kan maganar da yayi cewa Fulani Makiyaya na da hakkin rike bindigu don kare kansu.

A farkon makon nan gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa Makiyaya na rike bindigogi ne domin kare kawunansu daga masu satar shanu, suna kwashe muku dukiya.

Hira da jaridar Vanguard a Akure, gwamnan Ondo ta bakin kwamishanan labaransa, Donald Ojogo, yace Alla-wadai irin kalaman da gwamna Bala yayi.

  Yanzunnan Fada ya Barke Tsakanin Hausawa da Yarbawa a Lagas

“Idan da gaske ya fadi hakan kuma ya yarda, lallai gwamnan jihar Bauchi yayi magana a madadin gwamnatin tarayya kenan cewa ya halatta dukkan yan Najeriya, har da makiyaya, su rike haramtattun makamai irinsu AK don kare kansu,” yace.

“Abinda gwamnan ke kokarin fadi shine ko u yarda ko kada mu yarda, wajibi ne makiyaya su rike bindiga AK47 don kare kansu amma sauran yan Najeriya su zuba ido tsagerun yan bindiga na kashesu.”

“Da wannan kalaman da gwamnan Bauchi yayi, lallai mun shiga cikin wani sabon halin rikici kenan.”

“Bai cancanci rike kujeran mulki ba,mutane irinsa masu halaye irin nashi ba su cancanci mulkan jama’a ba.”

“Maganar banza yayi, kuma babu inda ya cancanci a jefar da kalaman illa kwandon shara.”