Tirkashi! Anyi dumu-dumu da wani ango tare da kawar amarya a ranar biki

Tirkashi! Wani abun al’ajabi ya afku a garin Port Harcourt inda aka kama ango yana tarawa da kawar amarya a ranar daurin aurensu

Advertisements
Advertisements

A cikin wani bidiyo da ya bazu a yanar gizo, an gano amaryar tana caccakar wanda ya kamata ya zama angon nata, inda ta bayyana cewa shine umul’aba’isin rusa farin cikinsu

Har ila yau abokan angon sun nuna rashin jin dadinsa yayinda suka daura laifin komai a kan abokin nasu

Wani aure ya mutu tun kafin a kai ga daura shi bayan amaryar ta gano cewa mijinta na mu’amala da babbar kawarta, jaridar The Nation ta ruwaito.

A bisa ga rahoton kafafen sadarwa, rigima ta barke a birnin Port Harcourt yayinda amaryar ta yiwa angon wankin babban bargo a tsakiyar hanya tana mai zarginsa da rushe auren.

  Matasa sun tayar da zanga-zanga a kofar mata yanzunnan-Kano

A cikin bidiyon wanda ya bazu a dandalin sada zamunta, an jiyo abokan angon suna fadin cewa ‘ka kwafsa’ bayan sun tabbatar da aikata ta’asar.

A wani lamari na daban, ‘Yar wasar fim, Grace Ifemeludike, ta ba mazan da su ke yaudarar matan aurensu shawarar su rungumi auren mata da yawa domin su daina lalata da mata.

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Daily Nigerian, Grace Ifemeludike wanda jarumar Nollywood ce, ta yi wannan kira ne a shafinta na Instagram.

Da ta ke magana a ranar Talata, 9 ga watan Fubrairu, 2021, Grace Ifemeludike, ta yi Allah-wadai da yadda zina ta zama ruwan dare tsakanin mazaje a Afrika.

  Momi Gombe Ta kama shiya fina-finai da auren wani akanta

A gefe guda kuma, wata mata mai aikin da’awah yaɗa addinin Kirista, Chinwe, ta yi watsi da ƙarar saki da aka kawo akanta a kotun gargajiya da ke zamanta a Igando Legas.

Ta kuma zargi mijinta Paul Ekwe, wanda fasto ne da aikita aikin assha da mata mambobin cocinsa kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Faston, wanda ya shigar da ƙara gaban kotun yana roƙon ta datse igiyar auren da ke tsakaninsu da matarsa Chinwe, ya zargeta da ƙulla makirci don ganin bayansa.