Taaddanci: Mun fatattaki yan Boko Haram a Najeriya

Babban Hafsan Sojin Najeriya, Tukur Buratai, ya bayyana cewa jami’ansa sun fitittiki yan ta’addan Boko Haram daga dukkan jihohin Arewa maso gabashin Najeriya face jihar Borno.

Advertisements
Advertisements

Buratai ya bayyana hakan ne yayinda ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari ranar Litinin, 10 ga Agusta, 2020, Premium Times ta gani.

Hafsan Sojan, ya kara da cewa yanzu haka jami’ansa na amfani da labaran leken asiri domin kawar da yan ta’addan daga Borno.

Mun fitittiki yan Boko Haram daga Arewa maso gabas, jihar Borno kawai suka rage - Buratai
Mun fitittiki yan Boko Haram daga Arewa maso gabas, jihar Borno kawai suka rage – Buratai

“Babu yan Boko Haram a sauran jihohin dake makwabtaka. An fitittikesu, yanzu suna boye a jihar Borno,”

“Muna aiki tare da masu fararen hula da sarakunan gargajiya, abinda muke bukata kawai shine hakuri. Ba zamuyi kasa a gwiwa ba.” ya bayyana a jawabin da kakakin Buhari, Garba Shehu ya fada.

  Wilfred Ndidi excluded from the list of the African best players of the year

Duk da wannan ikirari da Buratai ke yi, a watan Mayun nan yan ta’addan Boko Haram sun kai hari garin Dapchi, a jihar Yobe. Gabanin nan ma sun kai wani garin Babangida a jihar a watan Febrairu.

A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya daura laifin rashin samun nasarar yakin yan ta’addan Boko Haram a Arewa maso gabashin Najeriya kan rashin isasshen kudi a baitul malin gwamnati.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin ganawarsu da kungiyar gwamnonin yankin Arewa maso yamma a fadarsa dake Aso Villa.

Ya kara da cewa cutar Korona ce ta kara tsananta lamarin.

Amma ya ce akwai damuwa matuka bisa yadda matsalar tsaro ke tsananta fiye da yadda ya samu abin lokacin da ya dau ragamar mulki.

  "I never thought Emmanuel Amuneke like me for once in his life" says Victor Osimhen.

“Muna da matsalan rashin kudi da rashin tsaro. Kun san gado mukayi. Amma ya kamata Al’ummar Arewa maso yamma su godewa abinda gwamnatin nan tayi.”

“Ina tabbatar muku da cewa gwamnati na iyakan kokarinta. Rashin kudi ya zame mana kalubale.” Buhari yace