Sojojin Najeriya sun koka cewa ba Kanal Bako kurin suka rasaba a harin da aka kai musu

Dakarun soji sun nuna fushi kan wariya da aka nunawa sauran sojoji da suka mutu tare da Kanal Bako

Advertisements
Advertisements

Kanal Bako ya kasance kwamandan sashi 2 na Operation Lafiya Dole, rundunar da ke yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar

Yan Boko Haram ne suka kashe kwamandan tare da wasu sojoji a harin bazata da suka kai masu

Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi fushi sosai da mahukunta kan rashin karrama sauran sojojin da yan Boko Haram suka kashe tare da kwamandansu, Kanal Dahiru Bako, Shara Reporters ta ruwaito.

Kafin kisan nasa, Bako ya kasance kwamandan sashi 2 na Operation Lafiya Dole, rundunar da ke yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar.

  Boko Haram attacked military Barracks in Borno

Babban jami’in sojan ya rasa ransa a ranar Litinin, a wani harin bazata da yan ta’addan suka kai kansu, kamar yadda HumAngle ta ruwaito.

Sai dai an tattaro cewa ba a ambaci sauran sojoji uku da aka kashe tare da Bako ba balle a karrama su.

Sunayen sauran sojojin da aka kashe tare da kwamandan sune; Lance Corporal Oluwaseyi, Lance Corporal Nwobuji Desmond da Private Aliyu Ibrahim.

An ruwaito cewa babu wani sakon jaje daga hukumar sojin zuwa ga iyalan mamatan.

Wani makusanci, wanda ya zanta da HumAngle, ya bayyana cewa da hakan, hukumomin na ci gaba da nuna banbanci tsakanin wadanda ke karkashinsu da kuma gaza nuna jagoranci nagari.

  Dahiru Usman Bauchi, ya musanta goyon bayan Mailafia a kan ikirarinsa