Sojojin Najeriya: Gwamnan yace muje wajenda ake zanga-zangar endSARS- Lagos

Sojojin Najeriya, ta musanta harbin masu zanga-zanga a Lekki Toll Gate da ke Legas a ranar Talata, 20 ga watan Oktoban 2020, inda rundunar ta ce gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ne ya kira su domin zuwa wurin masu zanga-zanar ta #ENDSARS.

Advertisements
Advertisements

A wata sanarwa da mai magana da yawun runduna ta 81 ta sojojin da ke Legas, Manjo Osoba Olaniyi ya fitar, ta bayyana cewa:

“Rundunar sojojin Najeriya ta 81 ta ga wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta da yake nuna cewa sojoji sun kashe farar hula da ke zanga-zanga a Lekki.

”Wannan zargin ba gaskiya ba ne, kuma hakan na so ya jawo rashin zaman lafiya ne kawai a cikin ƙasa”, in ji rundunar.

“Sai dai gwamnan Legas ne ya yanke shawarar kiran sojoji domin kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa a ranar ta Talata bayan saka dokar hana fita ta sa’o’i 24.”

  Super Governor Zulum Condoles the families of the fallen heroes.

Wannan sanarwar ta sojojin na zuwa ne kwana bakwai bayan lamarin da ya faru a Lekki da ke Legas inda bayan nan ne aka fara samun rikice-rikice da suka haɗa da fasa rumbunan abinci a wasu jihohin Najeriya.

Me ya faru a ranar Talata da lamarin ya faru?

A ranar da lamarin ya faru, wasu da ake zargin cewa sojojin Najeriya ne suka buɗe wuta ga masu zanga-zangar #ENDSARS da ke Lekki a Legas.

Rahotanni sun bayyana cewa duk da dokar hana fita da aka saka a jihar ta Legas, masu zanga-zangar sun yi biris da dokar inda suka fita suka ci gaba da abin da suke yi.

Sai dai rikicin ya faru ne bayan da masu zanga-zangar suka fara jin harbe-harben bindiga, bayan lokaci kaɗan sai wurin ya yamutse .

Babu takamaimai adadin mutanen da suka samu rauni a wurin, sai dai gwamnan jihar ya ce aƙalla mutum 30 ne suka raunata.

  Momi Gombe Ta kama shiya fina-finai da auren wani akanta

Wasu da ke wurin sun bayyana cewa an kashe aƙalla mutum bakwai bayan da aka fara harbe-harben.

Me ya faru bayan lamarin da ya faru a Lekki?

Kwana ɗaya bayan faruwar lamarin, gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya bayyana cewa wasu da suka fi ƙarfinsa ne suka yi harbe-harben a daren Talata.

Da sanyin safiya gwamnan ya ziyarci asibitin da aka kai waɗanda suka samu rauni yayin lamarin, inda ya ce a ƙalla mutum 30 ne aka raunata.

Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta bayyana cewa binciken da ta yi ta gano cewa mutum 12 aka kashe a wurare biyu a Legas a ranar Talata.

An yi “kashe-kashen” ne a Lekki da Alausa, wuraren da dubban mutane suka jima suna gudanar da zanga-zangar kawo ƙarshen cin zarafin da ‘yan sanda ke yi a Najeriya.

  The first baby of the year was welcomed in Lagos.

Kafin sojojin Najeriya su musanta wannan zargin, gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya yi hira da gidan talabijin na CNN inda ya bayyana cewa daga bidiyon da ya gani, kamar sojoji ne suka yi wannan harbe-harben.

Tuni dai gwamnatin Legas ta kafa kwamitin bincike domin gano ainahin abin da ya faru a wurin.

Gwaman jihar ya bayyana cewa kwamitin da aka kafa zai yi amfani da bidiyon da kyamarorin da ke wurin suka ɗauka domin taimaka masa wurin bincike.

Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila wanda ɗan majalisar wakilai ne da ke wakiltar Legas, ya bayyana cewa sojojin ne suka aiwatar da kashe-kashen da aka yi a Legas.