Shugaba Muhammadu Buhari ya Amince da Karawa Ma’aikata Kudi da shekarun kammala aiki

Shugaba Muhammadu Buhari ya yarda da biyan albashi na musamman ga malaman makaranta

Advertisements
Advertisements

Har ila yau shugaban kasar ya kara wa malaman shekarun aiki daga 35 zuwa 40

Adamu Adamu, ministan ilimi ne ya sanar da hakan a yau Litinin, 5 ga watan Oktoba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da biyan albashi na musamman ga malamai.

Shugaban kasar ya kuma kara wa’adin shekarun aikin malamai daga shekaru 35 zuwa 40, jaridar This Day ta ruwaito.

Ministan ilimi, Adamu Adamu, ne ya sanar da hakan a yau Litinin, 5 ga watan Oktoba.

Ya bayar da sanarwar ne a cikin wani jawabi na musamman da ya karanto yayinda yake wakiltan shugaban kasar a wajen taron zagayowar ranar malamai ta duniya

  Rundunar sojin saman Najeriya ta dauki aniyar gano dalilin hadarin jiragen sama