Saurayin da ya kashe iyayensa, matarsa da kanwar matarsa ya mika kansa ga ‘yan sanda

Saurayin Bayan kashesu da yayi, ya boye na kwanaki biyu amma daga bisani ya mika kansa ga ‘yan sandan yankin

Advertisements
Advertisements

Ya ce iyayensa sun bashi wani fili a kwari wanda ba zai iya gina gida a kai ba, lamarin da yasa yayi aika-aikar

Wani matashi mai shekaru 28 wanda ake zargi da kashe iyayensa, matarsa da kanwar matarsa a yankin Kisoro da ke yammacin Uganda, ya mika kansa ga ‘yan sanda a ranar Lahadi, 27 ga watan Satumba.

Wanda y’all lashes lows nasa

Wanda ake zargin mai suna Gerald Ndikumukiza, mazaunin kauyen Kageyo da ke Busengo a ranar Alhamis da ta gabata, ya kashe matarsa mai shekaru 26 mai suna Maserina Mujawimana.

  Ummi Zee Zee: Kije ki kashe Kanki Base kin fada ba||Zaharaddin Sani

Ya kashe mahaifinsa mai suna Deogratious Sebitama mai shekaru 80, mahaifiyarsa mai shekaru 75 mai suna Bonconsira Nyiraguhirwa kafin ya kashe kanwar matarsa mai shekaru 20 mai suna Joan Nyiramahoro.

yansandan damn sucks kamashi

Bayan aikata laifin, Ndikumukiza ya boye amma ya bar wata wasika a inda yayi laifin inda ya rubuta, “Abinda kuke son gani.”

Wanda ake zargin dan asalin yankin Masaka ne inda yake aiki a matsayin lebura, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan yankin Kigezi, Elly Maate, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Talata, ya ce wanda ake zargin ya mika kansa ga ‘yan sandan yankin Kisoro kuma ya sanar da jami’an tsaro cewa yana tsoron kada a banka masa wuta.

  Kannywood: Masallacin da Gabon ta gina ya jawo rigima

Maate ya kara da cewa, wanda ake zargin ya tabbatar da cewa da kanshi ya kashe iyayensa, matarsa da kuma kanwar matarsa a kan rikicin fili. Ya ce sun bashi filin da ba zai iya gina gida a kai ba.

Wanda ake zargin ya ce duk da Masaka da ya tafi domin neman kudi, bai samu ba, hakan ce ta sa ya kashe ‘yan uwansa saboda fushi