Saurayi ya turawa budurwa N50k dan ta aminta suyi fira a twitter

Wani saurayi ya turawa budurwa zunzurutun kudi har naira dubu hamsin saboda kawai ta yi masa martani a sakon da ya aika mata

Advertisements
Advertisements

Mutane sunyi caa akan saurayi da budurwar , inda wani bangaren ke cewa matan Najeriya kwadayinsu yayi yawa, wasu kuwa suna fadin akasin hakan

Budurwar dai ta wallafa hotunan yadda ta kasance tsakaninta da saurayin Kan mutane ya rarrabu a shafin sada zumunta na Twitter, bayan wata budurwa ta bayyana cewa wani mutumi ya tura mata kudi har naira dubu hamsin (N50,000) saboda kawai ta mayar masa da martanin sakon da ya aika mata a shafin sadarwa.

Saurayi ya tura wa budurwa N50,000 saboda damar hira da ita da ta bashi a kafar sada zumunta

  Abdul-Jabbar Nasiru Kabara makaryaci ne inji Ganduje

Budurwar mai suna @_Matriach da ta wallafa hotunan hirar da tayi da mutumin da kuma sakon waya da aka aika mata na kudin da ya tura mata, ta ce:

wannan shine tattaunawar samarin biyu

“Kai ina matukar zama na mace.”

Wannan rubutu da tayi ya sanya wasu maza sun tada jijiyar wuya, suka dinga zagin mutumin, akan wannan abu da yayi na turawa mace kudi domin ya jawo hankalinta.

Wasu kuma sunyi caa akan matan Najeriya akan halayyarsu ta neman kudi a wajen maza, inda suka bayyana cewa wannan dalili ne ya sanya mazan Najeriya suka fi ganewa auro matan da ba ‘yan Najeriya ba.

Wani mai suna @MrOdanz cewa yayi: “Abin mamaki mutum ya turawa mace dubu hamsin saboda kawai ta bashi damar magana da ita a social midiya.

  Wani Jajirtaccen Dan Najeriya Ya Kirkiri Kafar Yanar Gizo Gizo Saboda Rage Zaman Banza

Ba za a koyawa ‘yan Najeriya da za su zo nan gaba irin wannan rashin hankalin ba.

Dole ne wannan haukan ya mutu tare da mu.”

Ita kuwa wata mai suna @1nigeriangirl cewa tayi:

“Daga yaya wannan dubu hamsin da ka bayar ta sanya turawa suke tururuwar sonka? Maza ka karbi Visa ka bar kasar nan.

Shi kuwa Yariman Dubai mai jiran Gado, Sheikh Hamdan bin Mohammed bin Rasha Al-Maktoum, ya nunawa duniya cewa ba komai bane idan ka zama mai adalci ga dabbobi.

Yariman ya daina amfani da wannan mota domin ya tabbatar da lafiyar wadannan tsuntsaye.