Rundunar yan sanda ta fatattaki yan ta’adda, jami’ai 2 sun rasa rayukamsu a Zamfara

Rundunar yan sanda a jihar Zamfara ta tabbatar da yin artabu da yan bindiga a ƙauyen Magami dake jihar Zamfara Ranar Asabar

Advertisements
Advertisements

Kakakin hukumar yan sandan yace an kashe musu jami’ai biyu sakamakon lamarin, yayin da yan bindiga da yawan gaske suka baƙunci lahira

Kwamishinna yan sandan jihar ya gargaɗi yan bindigan dake jihar su aje makamansu a zauna lafiya ko kuma su cigaba da ganin fushin hukuma

Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa ta kashe yan bindiga da dama ranar Asabar da daddare yayin da suka yi ƙoƙarin kai hari ƙauyen magami, ƙaramar hukumar Gusau, kamar yadda Premium times ta ruwaito.

  Dabarun da kungiyar ISWAP tayi wajen damke Abubakar shekau

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da kakakin yan sandan jihar, Shehu Muhammed, ya fitar a Gusau.

Yace: “Ranar Asabar da daddare, mun samu rahoton cewa yan bindiga sun shiga garin Magami da niyyar kaiwa al’ummar garin hari.”

Nan take kwamishinan yan sanda, CP Hussaini Rabiu, ya umarci jami’an yan sanda da suka haɗa da jami’an Operation Puff Adder da sukai ɗauki domin tabbatar da kare mutane da dukiyoyin su.”

“Jami’an sun kai ɗauki inda suka yi musayar wuta da maharan, a sakamakon haka an sami nasarar daƙile harin, yayin da adadi mai yawa na yan bindigan suka mutu, sauran kuma suka gudi da raunin harbi a jikinsu.”

“Biyu daga cikin jami’an mu sun rasa rayuwarsu a yayin da suke ƙoƙarin kare al’umma, amma babu wani farar hula da ya mutu a harin.” Inji shi.

  Sojoji 300 aka kora don sunki tunkarar yan boko haram

Kakakin yan sandan ya kuma bayyana cewa kwamishin ya ƙara tura wasu jami’ai na musamman domin su cigaba da duba dajin dake yankin da nufin kare sauran ƙauyuka da harin yan ta’adda.

Yace: “CP ya kira yi yan bindigan dake jihar ko dai su aje makaman su a zauna lafiya ko kuma su cigaba da fuskantar fushin hukuma.”

“Ya kuma roƙi jami’an yan sanda da su kare kansu kuma su kare mutanen dake yankin su daga dukkan wasu hare-haren yan bindiga.”

Source: Legit