Riga Kafin Corona: Akwai Alamu Na Nuna Cewa Ana San yiwa Musulinci Makarkashiya?

Riga Kafin Corona; Masana kiwon lafiya sun ce yaɗa jita-jita kan riga-kafin cutar korona ba ƙaramar illa ba ce ga al’umma.

Advertisements
Advertisements

Tun bayan da aka fara yi wa mutane allurar riga-kafin kariya daga cutar korona da ta addabi duniya, mutane musamman a ƙasashe masu tasowa irin Najeriya ke yaɗa jita-jita iri-iri kan riga-kafin.

Wasu daga cikin labaran jita-jitar da ake yaɗawa sun haɗa da cewa so ake a rusa Musulunci da Musulmai a faɗin duniya.

Sai dai a wata hira da BBC ta yi da Dr Umar Jibrin Madugawa, wani likita ɗan Najeriya da ke aiki a Landan, wanda aka riga aka yi ma allurar, ya ce jahilci ne ke sa wasu yaɗa jita-jita ta ƙarya.

Tuni dai aka fara yi wa mutane riga-kafin a ƙasashe irin su Burtaniya da Jamus da Faransa da Saudiyya da Rasha da Qatar da Kuwait da sauran su da yawa.

Dr Madigawa ya yi kira ga dukkan mutanen da suke tababa kan riga-kafin da su bai wa allurar muhimmancin gaske don su yarda a yi musu ita.

“Ya fi alheri ƴan uwana baƙar fata su samu a yi musu allurar maimakon su ƙare da kamuwa da cutar Covid-19. Don ita wannan cuta ba ruwanta da yanayin fatarka ko arziƙinƙa, idan ta zo gaba ɗaya za ta yi maka.

“Don haka ina kira ga mutane su guji yarda da yaɗa jita-jita da raɗe-raɗi marasa amfani da za su cutar da mutane,” in ji Dr Madigawa.

  Federal Government: Why Schools Should be Re-open-- Adamu Adamu