Nidai ku rabamu: Mijina sai tai sihiri yake juma’i da ni kullun

Nidai ku rabamu nace. Wata mata ta maka mijinta a kotu inda take neman kotun ta raba aurensu saboda yana amfani da Sihiri wajan Jima’I da ita.

Advertisements
Advertisements

Matar tace a duk sanda mijin nata ke Jima’i da ita sai ta suma.

Matar me suna Bukola Ejalonibu ta bayyana cewa, idan ta suma yawanci sai an kaita Asibiti.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya,NAN ya ruwaito cewa matar ta shigar da karar ne a kotun Mapo dake jihar Oyo.

Saidai mijin nata, Kolawole ya karyata zargin da ta masa inda yace bata da godiyar Allah duk da abinda yake mata.

Mai shari’a, Ademola Odunade ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya raba auren tare da baiwa matar rikon yara 2 da suke dashi sannan ya bukaci mijin ya rika bata Dubu 10 duk wata.

  Covid-19: Almajirai 193 suka kamu da cutar coronavirus a Kano