Neman Bakin Zaren Matsalar Tsaro Yaja Sheikh Abubakar Gumi Yashiga Daji Yayi Wa’azi

Neman bakin zaren matsalar tsaron da yankin arewacin Najeriya ya faɗa ta sa mutane da dama tunanin yadda za su ba da gudunmawarsu domin ceto yankin daga halin da ya tsinci kansa a ciki.

Advertisements
Advertisements

Malaman addini ma ba a barsu a baya ba, domin kuwa a baya-bayan nan ne fitaccen malamin Addinin Islama a Najeriya, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, ya bayyana cewa ƙarancin ilimi na daga cikin matsalolin da ke ƙara ta’azzara matsalar tsaro a yankin arewacin.

Wannan na daga cikin dalilin da malamin ya bayyana kan ƙaddamar da wani gangami na fita yankunan jihar ta Kaduna domin ilimantar da mazaunansu da kuma yi musu wa’azi.

Sheikh Gumi ya bayyana dalilinsa na shiga irin waɗannan yankuna da ke da matuƙar haɗari a wannan lokaci domin yin wa’azi.

Su waɗannan bayin Allah makiyaya da suke zaune a daji suna buƙatar wanda zai koyar da su addini, domin taimaka musu su fita daga jahilcin da suke ciki.

Domin kuwa wajibi ne ga duk wani ɗan adam ya san ubangiji kuma ya bauta masa in ji Sheikh Gumi.

Ya ƙara da cewa ya tabbata ɓarnar da suka shiga ciki rashin addini ne ya jefa su, domin addini saita ɗan adam yake rashin shi kuma ya jefa shi wata hanya ta daban.

Saboda mutumin da yake shaye-shaye, yake fyaɗe kuma yake ƙwace dukiyar mutane ta yaya zai san abubuwan da yake ba su da ce ba, sai da saiti irin na addini, to su kuma ba su da wannan saitin.

Sheik Gumi yace da zarar an koya musu addini to zai kange su daga wannan ɓarna da suke yo.

Da aka tambaye shi ko halin da suke ciki na da alaƙa da sakacin malaman addini Musulunci sai ya ce, “To ai malaman addini kamar ɗan sanda ne na gwamnati sai an biya shi zai yi wannan aiki, wane ne zai shiga daji ba a biya shi ba?, haƙƙin gwamnati ne ta tabbatar da ilimin waɗannan mutane”.

Malamin ya ce a baya ya taɓa irin wannan yunƙuri lokacin da yaje hukumar kula da koyar da makiyaya, suna da tsari da komai a lokacin amma abin da suka rasa shi ne kuɗin da za su riƙa ɗaukar malamai da su kuma suna biyansu.

Ya ƙara da cewa masu wannan sace-sace suna da iyayen gida da ke gefe, saboda a lokuta da dama waɗanda suke kama mutanen bai fi naira 30,000 ake ba su ba a kuɗaɗen fansar da ake ansa.

Gumi ya ce ba wata riba suke samu ba don haka in aka yi musu tayin natsuwa za su karɓa cikin gaggawa.

  Buhari: Aikin banza Shuka dusa a ruwa-Taaziya