NECO 2020: Hukumar shirya jarabawa ta kasa ta saki sakamakon bana

NECO 2020, Hukumar shirya jarabawar fita sakandare ta saki sakamakon jarrabawar bana

Advertisements
Advertisements

Shugaban hukumar, Farfesa Godswill Obioma ne ya bada sanarwar hakan a hedkwatar hukumar da ke Minna

Ya kuma sanar da cewa hukumar ta soke wasu cibiyoyin rubuta jarrabawar 12 a wasu jihohi saboda samunsu da aikata magudin jarrabawa

Hukumar Jarrabawa ta Kasa wato (NECO) ta fitar da sakamakon Jarrabawar Dalibai da suka kamalla babban sakandare wato SSCE, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sakamakon ya nuna cewa adadin daliban da suka samu nasarar samun credit a darrusa biyar ko fiye da hakan ya karu da kashi biyu cikin 100.

  Yanzunnan Fada ya Barke Tsakanin Hausawa da Yarbawa a Lagas

Shugaban hukumar, Farfesa Godswill Obioma ne ya sanar da hakan a Hedkwatar ta Hukumar NECO da ke Minna a Jihar Niger.

Hukumar ta kuma soke wasu cibiyoyin rubuta jarrabawa 12 saboda samunsu da hannu wurin tafka magudin jarrabawa.

Ya ce makarantun da aka hana rubuta jarrabawar sun hada da hudu a Jihar Adamawa, biyu a Kaduna, biyu a Katsina, daya a Taraba sannan daya a babban birnin tarayya, Abuja.

A wani labarin daban, kun ji kungiyar samari masu kishin aljihunsu da ake kira Stingy Men Association (SMAN) a turance tana samun bunkasa inda ake ta bude rassa a kasashen duniya daban-daban, BBC Hausa ta ruwaito.

A ranar Litinin 11 ga watan Janairun shekarar 2020 ne kungiyar ta bude shafinta na musamman a kafar Twitter da Facebook tare da tamburi a Najeriya.

  Dabarun da kungiyar ISWAP tayi wajen damke Abubakar shekau

Wasu kasashen Afirka sun bi sahun Najeriya sun bude rassan kungiyar a kasashensu, kasashen sun hada da Ghana, Liberia, Uganda, Malawi da Zambia.