Mutanen da abin ya shafa un kulle hanyar Kaduna Zuwa Abuja||Zanga-Zanga

Mutanen garin Gauraka a jihar Niger sunyi zanga-zanga sun tare hanyar Abuja zuwa Kaduna domin janyo hankalin hukuma ta taimaka musu

Advertisements
Advertisements

Mutanen sun tare titin suna kona tayoyi wadda hakan ya janyo cinkoson ababen hawa a kan titina

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun ce kimanin mutum 30 ne yan bindiga suka sace a garinsu kuma suna neman kudin fansa.

Wasu mazauna garin Gauraka da ke karamar hukumar Tafa na jihar Niger, a ranar Litinin sun tare titin Abuja-Kaduna suna zanga-zanga kan yawan sace mutane da ake yi a garin,The Cable ta ruwaito.

Garin na Gauraka da kan babban hanyar Abuja zuwa Kaduna ne.

  Dauda Kahutu Rarara ya gwangwaje jaruman kannywood 2 da motoci
Masu Zanga-Zanga Sun Tare Hanyar Abuja-Kaduna Kan Sace Mutum 30 Da Yan Bindiga Suka Yi
Masu Zanga-Zanga Sun Tare Hanyar Abuja-Kaduna Kan Sace Mutum 30 Da Yan Bindiga Suka Yi. Hoto: @thecableng

Masu zanga-zangar sun dakatar da zirga-zirgan motocci a kan titin yayin da suke kona tayoyi domin janyo hankulan mutane.

Mutanen garin na zanga-zangar ne domin sace wasu yan uwansu da yan bindiga suka yi.

Sun ce an sace kimanin mutum 30 daga garin kuma har yanzu suna hannun masu garkuwa inda suke neman kudi masu yawa kafin su sako su.

Masu zanga-zangar sun ce sun yi hakan ne domin janyo hankalin hukumomin da abin ya rataya a kansu bayan yan bindigan sun afka garin misalin karfe 1 na dare sun sace mutum 15.

Da ya ke magana yayin zanga-zangar, wani mazaunin garin mai suna Hassan Hassan ya ce yan bindigan sun afka garin misalin karfe 1.17 na dare sun sace mutum 15.

  Nidai ku rabamu: Mijina sai tai sihiri yake juma'i da ni kullun

Ya ce sun yanke shawarar yin zanga-zangan ne domin neman gwamnati ta kawo musu dauki a jihar Niger.

Wani mazaunin mai suna Dare ya ce a ranar Alhamis da ta gabata yan bindigan sun sace mutum hudu kuma suna neman Naira miliyan 10 kudin fansa.

Ya ce mutanen unguwar sun sanar da yan sanda amma an ce musu babu makamai da motocci da za a dakile harin.

Dakin karatun ba shi da nisa da wani otel inda fashewar gas ya kashe mutane hudu kwanaki biyu da suka gabata.

Otel din mai suna Conference Hotel inda abin bakin cikin ya faru mallakin tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel ne.

  Wasu Daga Cikin Matasan Najeriya Masu karancin Shekaru da Miliyoyin Kudi

Source: Legit