Musulmai Sun Fusata, Sun Bukaci Fasto Mathew Kukah ya Gaggauta Kaura Daga Sokoto

Musulmai sun fusata da wasu kalaman da Faston ya yi a bikin kirismeti. 

Advertisements
Advertisements

Ana zargin Kukah da jawo rikici, an bukaci ya nemi afuwa ko ya yi kaura. 

Babban faston darikar Katolika a kasar Sokoto, Mathew Hassan Kukah ya na fuskantar barazana bayan jawabinsa da ya yi na bikin kiremeti a 2020.

Kungiyar al’ummar Muslimi ta bukaci faston ya fito ya bada hakuri game da kalaman da ya yi, ta ce idan ba haka ba, ya yi gaggawa ya bar jihar Sokoto salin-alin.

Wata al’ummar musulmai da ke Sokoto sun fadawa Mathew Hassan Kukah ya daina sukar musulunci da kuma musulmai, Punch ta fitar da wannan rahoto.

Wannan magana ta fito ne daga kungiyar Muslim Solidarity Forum ta reshen jihar Sokoto a wani jawabi da ta fitar ta bakin mukaddashin shugabanta.

Farfesa Isa Maishanu ya maidawa Rabaren Mathew Kukah martani na jawabin kirismetin da ya yi, inda ya ce yana kokarin hada musulmai da kiristoci fada.

Muslim Solidarity Forum ta ce malamin addinin kiristan ya na wasa da karar da ake yi masa a Sokoto, har ta kai ya koma sukar musulmai bini-bini.

Kungiyar ta ce a 2020, Kukah ya jagoranci zanga-zanga na kisan wani Fasto a Sokoto, amma ya yi gum game da tarin Fulani da aka kashe a Taraba a 2018.

Maishanu ya tunawa Kukah abin da aka yi wa Musulmai a Kafanchan a 1987, Zango Kataf a 1992, Tafawa Balewa a 1991, 1993, 1995 da 2001, da Yelwa Shandam a 2004, da kuma Zonkwa da Jarkasa a 2011?”

Wannan kungiya ta Muslim Solidarity Forum ta nemi Faston ya nemi afuwar jama’a, ko ya fice daga Sokoto gaba daya.

Hakan na zuwa ne bayan jami’an DSS sun ce sun bankado yunkurin kawo rikicin addini a wasu jihohi.

A wata sanarwa da ta fitar kwanan nan, hukumar DSS ta ce ta fahimci akwai yunkuri da wasu jama’a ke yi na tada rikicin addini a kasar nan.

An ambaci jihohin Sokoto, Kano, Kaduna, Filato, Ribas, Oyo, da kuma jihar Legas a cikin wuraren da ake shirin tada zaune-tsaye.

  Yajin aiki: Ministan kwadago ya baiyana ranar da ASSU zata janye yajin aiki