Munirat Abdulsalam: Kar wanda ya kara kawo mini mijin aure

Munirat Abulsalam tayi watsi tare da watsawa wadanda ke temaka mata wajen samun mijin aure kasa a ido.

Munirat Abulsalam tayi watsi tare da watsawa wadanda ke temaka mata wajen samun mijin aure kasa a ido.

Advertisements
Advertisements

Ta dauki kokarin da sukeyi a matsiyin cin fuska tare da cin zarafin kimar ta a matsayin mace.

Munirat tayi gargadi me zafi a wani tattaunawa da tayi jiya da misalin karfe 7:00 nayamma a kafar sada zumuntarta na youtube.

Tayi nuni da cewa ita ba kowani namiji ne ke iya zama mijinta ba, ta kuma zano abubuwan da take bukatar mijinta ya kasan ce dasu.

Munirat Abdulsalam

Ba inda yafi jan hankali akan abubuwan da ta lissafa shine “bana son namiji me bita zaizai da zargi”

“Ina son namijin da yasan duniya kuma yayi tafiye-tafiye tare da sanin minene ya dace da rayuwa da zamantakewa.

“Dole mijina ya zama yasan Book ya san littafi domin ni ina da son karatu sosai.

“Ya zama dole mijina ya barni nayi sana’a domin ni ba irin matannanne da se anbasu ashirin talatin ba.

Related Post

A satin da ya gabata ne babbar yar wasan kwaikwayon nan wato Munirat Abdulsalam ta shiga cikin tashin hankali inda wasu daga cikin magiya bayanta suka kafurta ta.

Labari ya bazu ko ina a kafafen yada labarai cewa “ta fita daga musulci alhali n ba abinda take nufi ba kenan”.

Bayan kwana daya da yin hakanne se ta fitar da wani video me tsawon minti ishirin da wani abu inda take karyata su harda kuka

Munirat Abdulsalam lokacinda taketa kuka tana karyata wadanda suka kafurta ta

Wannan ne ya bata damar fitowa kiri kiri take nuna raayinta akan irin mijinda take so ta aura tare da watsawa Datti assalafy kasa a ido.

Dattai assalafy yana daya daga cikin mutanen dake kokari dare da rana wajen nemawa Munirat mijin aure amma daga bisani se ta kisu.

Datti Assalafy

Wannan shine abinda ya fara da kuma raayin Munirat Abdulsalam.