Ministan Fasaha Yace Za’a Koyawa mutane 13,000 Aikin Yi

Ministan Fasaha Yace Za'a Koyawa mutane 13,000 Aikin Yi

Ministan kimiyya da fasaha yace mutane za su samu abin yi ta tsarin ESPWP

Advertisements
Advertisements

Ogbonnaya Onu ya ce gwamnatin tarayya za ta koyawa mutane 13, 000 aiki

Ministan ya roki kamfanoni da su dauki matasan aiki bayan sun samu horo

Ministan kimiyya da fasaha na kasa, Dr. Ogbonnaya Onu ya ce gwamnatin tarayya za ta inganta rayuwar matasa 13, 000 a Najeriya.

Ministan yana cewa za a dauki wadannan matasa aiki a bangarori uku na gwamnati da ake da su.

Ministan ya bayyana haka ne a garin Abakaliki, jihar Ebonyi, wajen kaddamar da shirin daukar aikin ESPWP da gwamnati za ta yi.

Dr Onu ya ce an kawo wannan shiri ne domin inganta ayyukan kananan hukumomi, jihohi da gwamnatin tarayya a kasar.

Related Post

Dr. Onu ya cigaba da cewa amfanin wannan shiri da gwamnatin APC ta dauko shi ne a tabbatar da dorewar ayyukan da gwamnatin ta ke yi.

A kowace karamar hukuma aikin da za ayi ya sha ban-bam, amma makusudin shi ne tabbatar ana yin ayyukan gwamnati da kyau, kuma suna dorewa. Inji Onu.

Ministan a jawabinsa, ya yi kira ga wadanda za su amfana da wannan shiri su nuna jajircewarsu da nufin su samu abin dogaro.

Bayan haka, Onu ya roki ‘yan kasuwa masu zaman kansu, su dauki matasan da za horas aiki bayan sun samu kwarewa da sanin makaman aiki.

A jawabin da Ministan ya gabatar gaban jami’an gwamnatin Ebonyi da NDE, ya ce gwamnatin tarayya za ta sa ido a game da yadda ake dabbaka shirin.