MC Tagwaye ya auri Maryam Uwais ‘yar mai bai wa Buhari shawara

Fitaccen mai barkwancin nan wanda yake kwaiwayon maganganun Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, Obinna ‘MC Tagwaye’ Simon, ya auri ‘yar Maryam Uwais, mai bai wa shugaban kasar shawara kan shirin kyautata rayuwar jama’a.

Advertisements
Advertisements

MC Tagwaye, wanda dan kabilar Ibo ne, ya auri Hauwa ranar Asabar, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram. Kauce wa Instagram,

Karshen labarin da aka sa a Instagram, 1

“Ga mutanen da suke tambaya…. mun yi aure cikin farin ciki yau… godiya,” in ji Obinna ‘MC Tagwaye’ Simon.

Ita ma Maryam Uwais, ta tabbatar da auren a shafinta ta Instagram inda ta wallafa hotunan daurin auren.

Ya taɓa haɗuwa da shugaban kasar, wanda ya shi kansa ya sha yin dariya idan ya saurari yadda MC Tagwaye yake kwaikwayon maganganunsa.

Related Post

“Ɗiyata, Hauwa, ta yi aure yau. Kuma na samu sabon ɗa, MC Tagwaye,” in ji ta.

Ta yi kira ga abokan arziki da sauran al’umma su yi wa sabbin ma’auratan addu’ar zaman lafiya da kariya daga Ubangiji.

MC Tagwaye ya shahara ne sakamakon kwaikwayon maganganun Shugaba Buhari, inda yake magana tamkar shugaban.

MC Tagwaye dan asalin jihar Anambra ne da ke kudu maso gabashin Najeriya, kuma yana yin sana’ar gabatar da jawabai na barkwanci musamman a wuraren bukukuwan aure.

Ya taba shaida wa BBC cewa ba Shugaba Buhari kadai yake kwaiwaya ba.