Matashiyar Budurwa: Tana neman saurayin Aure, idan akwai me sha’awa

Matashiyar budurwar ta wallafa wani kyakkyawan hotonta a shafinta na Twitter sannan ta tambayi mabiyanta ko suna bukatar matar aure

Advertisements
Advertisements

Tuni bangaren sharhi na wallafar tata ya cika da martani daga mazan Najeriya wadanda suka nuna ra’ayi a kanta

Wata likita daga yankin arewacin Najeriya ta je shafin soshiyal midiya don neman mijin aure, ta wallafa hotonta a shafinta na Twitter sannan ta tambayi mabiyanta ko suna bukatar matar aure.

Dr. Halima Abubakar tare da shafin Twitter @DrHalima_ ta sa mabiyanta tattaunawa kan kyakkyawan hotonta wanda ta wallafa tare da rubutu kamar haka:

“Wa ke bukatar matar aure?”

Wani mai amfani da Twitter @AHMEDJEEKA ya rubuta:

  Olusegun Obasanjo ya bayyanawa matasa yanda zasu karbe mulki a hannun tsaffi

“Ina ganin ba daidai bane tallata kanki a idon duniya kina neman abokan rayuwa, haramun ne a Musulunce.

Mutum irina ina bukatar matar aure amma da irin wannan tallar, ina tsoro.”

@makoloumar1 ya wallafa:

“Shin za ki auri talaka mai kishin nema?

Zan iya ciyar dake da baki kulawa sannan zan ba farin cikinki da kwanciyar hankalinki muhimmanci.”

@HerbertTruth ya yi martani da:

“Ina a hanyar zuwa gidan mahaifinki. Zan zo da magabata na yanzu haka. Babu lokaci.”