Matasa sun tayar da zanga-zanga a kofar mata yanzunnan-Kano

Matasa na gudanar da zanga-zanga a Kano kan mutuwar wani matashi a hannun yan sanda

Advertisements
Advertisements

An tattaro cewa yan sanda sun kama matashin mai suna Saifullahi a ranar Lahadi

Sai dai ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar, Abdullahi Haruna ba a kan lamarin

abinda ya faru kenan bayan mutuwar yaron da yansanda suka kulle

Dandazon matasa a Kano sun hau titunan jihar domin yin zanga-zanga sakamakon kisan wani matashi da ake zargin yan sanda da aikatawa.

Kungiyar Amnesty International ta bayyana matashin a matsayin Saifullahi mai shekaru 17, ta ce an azabtar da shi har lahira.

An tattaro cewa yan sandan sun kama matashin a ranar Lahadi, yayinda suke bin wasu da ake zargi da aikata laifi.

  Coronavirus: covid-19 will soon be isolated in Kano state--Ganduje

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa zanga-zangar ya fara ne lokacin da yan sanda suka dauki gawar Saifullahi zuwa gidan iyayensa a safiyar ranar Litinin.

“Masu zanga-zanga sun kewaye hanyar Kofar Mata sannan suka kona tayoyi inda suke wakokin kira ga kawo karshen cin zalin yan sanda,” in ji kungiyar.

Ba a samu jin tab akin Abdullahi Haruna, kakakin rundunar yan sandan jihar ba kan lamarin, domin bai amsa kiran wayar da aka masa ba.

Lamarin na zuwa ne a yayinda ake tsaka da zanga-zanga kan cin zalin da yan sanda ke yi wa al’umma a fadin kasar.

A wani labarin kuma, ministan tsaro, Bashir Magashi, ya ja kunnen matasan Najeriya akan kada su keta iyakar tsaro sakamakon zanga-zangar rushe SARS duk da gwamnatin tarayya ta fahimci manufarsu.

  Jerin Kasashen duniya 10 da suka fi kowace kasa hadari ta ko ina

Magashi yayi wannan kiran ga matasa a wata takarda da kakakin ma’aikatar, Mohammad Abdulkadri ya saki, kamar yadda jaridar Premium times ta ruwaito.

Ma’aikatar ta yi wannan jan kunnen a lokacin da shugaban kamfen din Buhari, Danladi Pasali, ya jagoranci wakilai a ma’aikatar tsaro dake Abuja.