Manyan Kano da kungiyar MURIC sun yabi zabin Ganduje akan Abdul-Jabbar

Manyan Kano da Kungiyar MURIC ta yabi Gwamnan Kano na dakatar da Abduljabar Nasiru-Kabara

Advertisements
Advertisements

Muslim Rights Concern ta ce Gwamnati tayi daidai da aka hana malamin yin karatu

MURIC ta bukaci a bude makarantar Shehin idan ya amince zai daina barambarama

Kungiyar nan ta Muslim Rights Concern watau MURIC ta yabi gwamnatin Kano a kan dakatar da Sheikh Abduljabar Nasir-Kabara daga yin wa’azi.

MURIC ta fitar da jawabi wanda shugabanta, Ishaq Akintola, ya sa hannu. Jaridar The Cable ta fitar da wannan rahoto a ranar 7 ga watan Fubrairu, 2021.

Farfesa Ishaq Akintola ya ce gwamnatin Abdullahi Ganduje ta yi maganin matsalar da wuri.

  Gwamnatin jihar katsina ta ceto kimanin mutane 103 a hannun miyagu

Ya ce: “An dade ana kuka da irin karatun da Sheikh Abduljabar Kabara yake yi, kungiyoyin Tijaniyyah da sauran Musulmai ‘yan Ahlul-Sunnah sun koka da shi.”

“Har ma su na zargin shi da zagin Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW).

Wannan abu ne da zai iya jawo Kano da sauran yankin Arewa su barke da rikici.”

“Mun yaba wa gwamna Ganduje da ya yi wa lamarin rigakafi.

Hakan zai taimaka Yanzu ba lokaci ba ne da za a bar rikicin addini ya barke.” Inji Farfesa Ishaq Akintola.

Kungiyar ta ce: “Miyagu na nan su na jira rigima ta kaure domin su samu damar yin ta’adi.

Za su yi amfani da wannan dama ne su jawo rashin zaman lafiya.”

A dalilin haka ne MURIC ta ke ganin gwamnan Kano ya cancanci yabo.

  FG Ta amince ta biya ma'aikatan N-power rukunin A & B kudadensu

“Mu na fatan sauran gwamnoni za su tashi tsaye, su yi maganin duk wata rigima.”

“Mu na kira ga gwamnatin Kano ta bude masallacin Sheikh Kabara idan ya amince da cewa zai bi doka, zai guje wa yin hudubobi da za su tunzura al’umma.”

Shi ma tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya yi magana a kan dambarwar Sheikh Abduljabbar Kabara da gwamnati da malaman jihar Kano.

MURIC ta bukaci a bada sharuda wajen mukabalar da za ayi, sannan ta ba gwamnati shawara ka da a haska shirin kai-tsaye domin gudun martani daga jama’a.

Malam Muhammadu Sanusi II ya bayyana abubuwan da su ke faru wa a Kano da fitintinu, ya roki Ubangiji ya kawo mafita, tare da kiran mutane su bi koyarwar Sunnah.

  Wani Jajirtaccen Dan Najeriya Ya Kirkiri Kafar Yanar Gizo Gizo Saboda Rage Zaman Banza