Manchestar kauye da manchestar birni : wasanda yafi ko wane wasa zafi a firimiyar ingila.

Machestar birni da ta kauye zasu kara da misalin karfe 5:30 na yammacin yau asabar a mako na 16.

Advertisements
Advertisements

An sami chanje-chanje dayawa tsakanin kungiyoyin biyu, kuma ya banbanta wasannin da suka kasance tsakaninsu a lokutan baya.

Dan wasan tsakiya na manchestar birni wato Gundogan ya sauyo zuwa filin taka leda baya wata dakatarwa da akai masa kwanakin baya kuma hakan ya jawo tsaiko daga nasarorin da kungiyar ke samu tin a baya.

Amma kuma daya daga chikin manyan yanwasan birnin wadanda suke kusa da raga wato Sergio Aguero baze samu damar buga wasanba ko maye dalili? oho.

Related Post

A gefen kungiyar Manchestar kauye kuwa, an dan sami chanji suma kamar takwararta ta birni, ta inda zakuga chewa dan wasan gaba na Manchestan wato Martial ze sami damar buga wasan dukda dukda cewa yasha fama da rauni a makonnin da suka gabata, kuma shine ma dalilin rashin buga wasan Tottenham.

Shiko dan wasan gaban na kusa da raga dan kasar faransa wato Poul Pogba vaze sami damar buga wasan ba sakamakon raunin da yake dashi na mako da dama, ze chigaba da kasancewa a benchi.