Kungiyar nan ta ASSU ta bayyana cewa, bazasu janye yajin aiki ba anan kusa

Ade Adejumo na gungiyar ASSU ya musanya maganar da Gwamnatin Tarayya ta yi kwanan nan

Advertisements
Advertisements

Farfesan ya bayyana abin da ya sa su ke yajin-aiki da kuma abin da su ke nema

A ranar Laraba, 30 ga watan Satumba, kungiyar ASUU ta malaman Jami’an Najeriya ta yi magana game da yajin-aikin da ta dauki tsawon lokaci ta na yi.

ASUU ta bayyana cewa ba ta da shirin janye yajin-aiki har sai gwamnati ta biya ta bashin albashin watanni uku zuwa bakwai da malaman jami’a su ke bi.

Bayan haka, ASUU ta ce dole a amince da manhajar UTAS da su ka kawo domin a rika biyan albashin malaman jami’o’i, idan ana so a bude makarantu.

  Mother of 13 Children gave birth to 4 kids again in Zaria

Jaridar Business Day ta rahoto Farfesa Ade Adejumo, wanda shi ne shugaban kungiyar ASUU na reshen Ibadan, ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar.

Kungiyar malaman ta karyata Ministan kwadago, Chris Ngige, na cewa yajin-aikin da ake yi ya kusa zuwa karshe, Farfesa Ade Adejumo ya ce ko kusa.

Farfesan ya ce gwamnati ba ta cika alkawuran da ta yi ba, daga ciki akwai batun alawus, yarjejeniyar 2009, inganta jami’o’i da kuma karin albashi.

Ade Adejumo ya ce abubuwa uku su ka sa ASUU ta tafi yajin-aiki, manufofin gwamnatin tarayya na rashin tausayi, watsi da harkar ilmi da karya alkawari.

  Donald Trump is Been Barred From Entering Scotland
ASUU ta yi kaca-kaca da Buhari, Minista, ta ce ta shafe watanni 7 babu albashi
Shugabannin ASUU da Ministan kwadago Hoto: Labor NG

Adejumo ya ke cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari mai-ci, ta ba ASUU kunya, domin kuwa sun yi tunanin za ayi yaki da rashin gaskiya a Najeriya.

Jagoran na ASUU ya ce gwamnatin APC ta raina malaman jami’a, sannan ba ta damu da sha’anin ilmi ba. Ya ce sai an biya masu bukatu kafin a bude makarantu.

Ngige ya kuma bada tabbacin cewa kwanan nan kungiyar ta ASUU za ta janye yajin aikin nata.