Kungiyar matan gwamnoni sunyi gangami akan matsalar rashin Tsaro a kasannan

Ƙungiyar matan gwamnonin ƙasar nan, sun nuna matuƙar damuwarsu da halin rashin tsaron da talakawa ke ciki

Advertisements
Advertisements

Shugabar ƙungiyar, Bisi Fayemi, itace ta bayyana haka a Abuja, jim kaɗan bayan fitowa daga taron da suka gudanar

Tace ita da sauran yan uwanta zasu haɗa ƙarfi da karfe tare da taimakon mazajen su wajen inganta rayuwar talaka

Matan gwamnonin ƙasar nan ƙaraƙashin ƙungiyarsu sun bayyana matuƙar damuwarsu kan karuwar matsalar tsaro a faɗin Najeriya tare da talaucin da ya addabi yan ƙasa, kamar yadda punch ta ruwaito.

Saboda haka, matan sun bayyana cewa zasu haɗa hannu da mazajen su, Gwamnoni, domin magance duk wani ƙalubalen da ya taso.

  Kannywood: Maryam AB yola ta sanar da fitar ta daga kunyar shirya fina-finai ta arewa

Shugabar ƙungiyar, Bisi Fayemi, matar gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ita ce ta bayyana haka ga manema labarai jim kaɗan fitowar su daga taro a sakateriyar NGF dake Abuja.

UGC Tace: “Muna matuƙar damuwa da halin tsaron da ƙasar mu ke ciki, da kuma mummunar shafan mata da ƙananan yara da yanayin yayi.”

“Hakanan kuma mun damu da yawaitar rashin aikin yi, wanda yasa matasa ke zaman kashe wando, babu aikin yi.”

“Sannan mun damu da talaucin da ya addabi mata musamman waɗanda ke rayuwa a ƙauyukan ƙasar nan.”

Mrs. Fayemi ta ƙara da cewa yan uwanta matan gwamnoni a shirye suke su taimakawa gwamnatocin jihohin su domin ganin an samar da rayuwa mai inganci ga yan ƙasa.

  ASUU ta amince zata janye yajin aiki, an karawa musu N10bn

Tace ita da sauran takwarorin ta zasu yi dukkan mai yuwu wa tare da haɗin guiwar mazajen su domin tabbatar da an inganta rayuwar talaka.