Koriya ta aikowa Najeriya kyautan rumfar gwajin cutar Korona na zamani

Yayinda hukumar NCDC ke kukan an daina gwaji, kasar Koriya ta aikowa Najeriya babban kyauta

Advertisements
Advertisements

Yanzu yan Najeriya za su iya shiga rumfa ayi musu gwaji ba tare da bata lokaci ba

An yi bikin amsar kyautan a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis

Gwamnatin tarayya ta karbi kyautar rumfar gwajin cutar Korona na zamani guda uku daga hannun gwamnatin kasar Koriya.

Kasar Koriya ta baiwa Najeriya kyautan rumfunan ne ranar Alhamis a Abuja domin kasar ta kara karfin karban samfuri da yiwa mutane gwajin cutar.

Dirakta Janar na hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC, Chikwe Ihekweazu, yayin karban kayayyakin ya ce lallai rumfunan zasu taimakawa Najeriya wajen kara yawan gwajin cutar.

  Kannywood: Matashi Musa Abdullahi, ya canzo shiri akan Maryam Yahaya

Diraktan harkokin wajen kasar Koriya, Woochan Chang ya yabawa gwamnatin Najeriya bisa kokarinta wajen dakile annobar.

“Wadannan rumfunan gwajin zasu taimaka wajen kare ma’aikatan lafiya yayin karban samfuri, kuma zasu taimaka wajen kara adadin gwajin cutar cikin kankanin lokaci,” Chang yace.

Karamin Ministan lafiya, Adele Mamora, wanda ke hallare a taron ya godewa gwamnatin Koriya bisa gudunmuwar da take baiwa Najeriya domin karfafa yakin da take kan Korona.

Minista Sadiya ta auri babban hafsan mayakan Sojin sama, Sadiq Baba A bangare guda, Hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 111 a fadin Najeriya.

  Emir of Kano and hundreds more Escaped plane Crash || soccarnews

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:na daren ranar Talata 22 ga Satumba, shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 176 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Lagos-31

Gombe-18

Kaduna-18

FCT-15

Rivers-14

Imo-3

Kwara-3

Oyo-3

Bayelsa-2

Ogun-2

Edo-1

Osun-1

Jimillan wadanda suka kamu: 57,724

Jimillan wadanda aka sallama: 48,985

Adadin wadanda suka yi wafati: 1,102