Kisan Gilla: Hauwa’u ta zayyana Dalilinda yasa ta kashe ‘ya’yan Cikinta

Hauwa'u matata ce kuma kishinta ya sanya ta kashe mani yaya haka kurin saboda zan kara aure, wanda a addinance ma be mharamta ba.

Hauwa’u matata ce kuma kishinta ya sanya ta kashe mani yaya haka kurin saboda zan kara aure, wanda a addinance ma be mharamta ba.

Advertisements
Advertisements

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kisan kan da wata matar aure ta yi a jihar

Mahaifiyar ‘ya’ya biyu mai suna Hauwa a jihar Kano ta yi wa ‘ya’yanta yankan rago da safiyar Asabar

An gano cewa, hakan ta faru ne sakamakon tsananin kishi da take a kan mijinta ya kara aure

Mamarsu tayi musu yankan Rago saboda zafin kishi

Wata matar aure mai suna Hauwa da ke zama a kwatas ta Diso da ke karamar hukumar Gwale ta jihar Kano ana zarginta da yi wa ‘ya’yanta biyu yankan rago.

Hakan ta faru bayan rikicin da ya auku tsakaninta da mijinta mai suna Ibrahim Haruna Aminu wanda bai dade da yin sabuwar amarya ba.

Jaridar Solacebase ta wallafa cewa, yaran da mahaifiyarsu ta yi wa yankan ragon su ne Yusuf Ibrahim mai shekaru 5 da kanwarsa Zahra’u mai shekaru uku.

Wani kawun yaran, Sadiq Haruna Aminu, ya ce Hauwau wacce matar dan uwansa ce kuma mahaifiyar yaran, tana rayuwa cike da hassada da kishi tun bayan da dan uwansa ya auro wata matar, lamarin da yasa ta kashe ‘ya’yanta biyu a ranar Asabar.

Related Post
Hauwa’u Kenan wacce ta sossokawa yayanta wuka da safiyar jiya sabon tsabar kishi

“Hauwa ta sossoka wa ‘ya’yanta wuka wanda hakan ya kawo ajalinsu,” Sadiq Aminu yace.

Dagacin Diso, Malam Ahmad Bello, ya nuna razanarsa da aukuwar lamarin ga manema labarai a jihar Kano a ranar Asabar.

Ya ce hakan ta faru ne bayan mahaifin yaran baya nan ya tafi gidan amaryarsa a safiyar Asabar.

Bello ya kushe wannan lamarin, inda yace a maimakon ta kai lamarin kotu, sai ta yanke hukuncin kashe ‘ya’yanta da kanta.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna yace rundunar ‘yan sandan ta fara bincike.

Amma kuma an tabbatar da cewa, har yanzu ba a ga mahaifiyar ba domin ta tsere.

Domin nishadin masu karatu, ga wani labarin soyya me chike da chakwakiya da kuma alhini daga da 1 zuwa na 5, su kudda poton da kuke bukata domin jin abinda labarin ke cewa, mun gode

Idan akwai bukatar aji karshen labarin da matsalolin dake cikinsa to se a danna SUBSCRIBE tare da latsa karaurawa domin sanarwa idan an dora chigabansa

NA WAYE??? KASHI NA DAYA
NA WAYE??? KASHI NA BIYU
NA WAYE??? KASHI NA UKU
NA WAYE??? KASHI NA HUDU
NA WAYE??? KASHI NA BIYAR