Kannywood: Matashi Musa Abdullahi, ya canzo shiri akan Maryam Yahaya

Musa Abdullahi, matashin nan mai matukar son ‘yar wasar kwaikwayon Kannywood, Maryama Yahaya, wanda ya sha guba don rashin ganinta ya sake komawa jihar Kano domin cika burinsa.

Advertisements
Advertisements

Daily Trust ta samu zantawa da shi a wannan karonn jin ta bakinsa kan dalilin da yasa ya kusa hallaka kansa don wata ‘yar Fim.

Matashin yace ko kadan bai yi nadamar shan maganan kwari ‘Sniper’ ba saboda bakin cikin rashin ganin jarumar da ya dade yana shaukin gani.

Ban yi nadamar shan guba don ita ba. Nadamar da zan yi shine idan na kasa ganinta.”

Ya ce abokansa da suka bashi masauki a baya sun yi hannun riga da shi saboda tsoron abinda ya aikata a baya.

  Rahama Sadau tayi cikakken bayani akan muradin Zuciyar ta

Shugaban kungiyar yan wasan kwaikwayo na jihar Kano, Malam Alhassan Kwalle, ya ce yaron ne yayi ba daidai ba na rashin sanar da jarumar niyyarsa kafin zuwa Kano da farko.

“Lokacin da yaron yazi, bai wurin wanda zai je ya hada shi da Maryam Yahaya ba kuma saboda irin matsalar rashin tsaron da ake ciki, babu mai hankalin da zai bari wani da bai sani ba ya zo ya ganshi.

“Saboda haka, babu wanda ke shirin kai shi ganin jarumar.” Kwalle yace

Yayinda aka tambayeshi shine ya samu ganinta yanzu da ya dawo, Abdullahi ya ce a’a.

A watan Yuli, Legit ta kawo muku rahoton cewa wani matashi da ya zo daga Yobe ya sha fiya-fiya saboda bai samu ganin Maryam Yahaya ba.

  Momi Gombe Ta kama shiya fina-finai da auren wani akanta

Abdullahi ya yi tattaki tun daga jihar Yobe da ke yankin arewa maso gabas na kasar nan, don ganin jaruma Maryam Yahaya, ya so yayi ajalin kansa saboda rashin cikar burinsa na ganin jarumar ta shi.

Kamar yadda jama’ar da ke wurin suke bayyanawa, matashin ya kwana a Unguwar Zoo road, inda ya zama kamar dandalin taruwar jaruman Kannywood don ya ga jaruma Maryam Yahaya amma bai samu ganin ta ba.

Hakazalika, an ji wasu na cewa sau uku matashin ya yi yunkurin shan fiya-fiya, kafin daga bisani ya bulbulawa cikin sa maganin kashe kwari da ya kusa zama ajalinsa.

An dai samu ceto rayuwar matashin ta hanyar bashi agajin madara.

  Yanzunnan Fada ya Barke Tsakanin Hausawa da Yarbawa a Lagas

Sai dai duk da wannan abu da ke faruwa, Jaruma Maryam Yahaya bata san yana yi ba ko kuma ta yuwu bata samu koda labari ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: