Kannywood: Maryam AB yola ta sanar da fitar ta daga kunyar shirya fina-finai ta arewa

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Maryam AB yola, ta fitar da sanarwa a shafinta na Instagram inda tace daga ranar 1 ga watan Satumban 2020, ta bar masana’antar Kannywood.

Advertisements
Advertisements

Daga karshe ta mika godiyarta ga masoyanta, kawaye da abokan arziki a kan irin kaunar da ake gwada mata.

Kamar yadda ta wallafa a shafin nata, “Assalamu alaikum. Ni Maryam AB Yola ina mai sanar da ku cewa daga yau daya ga watan Satumban 2020, na daina yin fim kuma na bar Kannywood

Maryan AB yola tsohuwar matar adam a zango ta bar kannywood tareda zayyanawa doniya cewa bata ba kannywood.

“Kuma ina matukar godiya da kaunar da kuke nuna min. Allah yasa mu dace, Ameen.”

Jarumar wacce tsohuwar mata ce ga fitaccen jarumi Adam A. Zango, mazauniya garin Abuja, bata sanar da dalilinta na yanke wannan hukuncin ba.

  BUHARI yafi kowa ma biya a tiwita-3121169

Ta wallafa sanarwar ne a bangaren saka labari na shafinta na Instagram, inda babu damar a yi tsokaci kowa ya gani. Yin tsokaci a kai zai shiga kai tsaye ne ya sameta.

A wannan shekarar, kusan jarumai mata uku ne suka sanar da ficewarsu daga masana’antar Kannywood ba tare da sanar da dalilinsu ba. Ta yuwu aure ne ko karatu dalilin, Allah kadai ya sani kuma lokaci zai nuna.

A baya-bayan nan ne jaruma Halima Abdulkadir, wacce aka fi sani da Intisar, ta sanar da daina fim dinta ba tare da wani bayani ko dalili ba.

Hakazalika, jaruma Asma’u Nass ta yanke wannan shawarar duk da bata wallafa a shafinta ba, amma ta sanar da makusantanta a masana’antar, tashar tsakar gida ta ruwaito.

  Adebiyi Ya Sanar da Ranar Kammala Titin Abuja-Kaduna-Kano

A shakarar 2018, jaruma Maryam Mah ta sanar da ficewarta daga masana’antar, hakazalika jarumar Aisha Umar Muhammad, wacce babu dadewa da bada wannan sanarwar aka ji aurenta kwatsam.

Kafin daina fim din jaruma Maryam AB Yola, ta fito a fina-finai irinsu Nass, Alkawari, Hafeez, Wutar Kara, Ramakon Gayya da sauransu.