Rama sadau: An gano wanda yai rubutu a hotonan jarumar kannywood

Rahama sadau ta kasance cikin tashin hankalin da barazar tinkarar shari’a sakamakon batanci da wani yayi a hotonta.

Advertisements
Advertisements

Kafafen watsa labarai da sada zumunta sun dauka, babu abinda kakeji da gani se maganar wannan batanci.

Harwa yau Rahama Sadau bata yarda cewa wanda yayi wannan aika aika yana da alaka da ita ba ko kuma da shirye-shiryen ta.

Rahama Sadau

Jarumar ta fito fili ta amsa laifinta na saka hotunan da tayi a sashenta na instagram kuma tayi na dama ta kuma bawa dukkan daukacin musulman duniya hakuri tareda alkawarin hakan baze sake faruwa ba.

Dukda hakan hukumar yansan da nata fadi tashi dan ganin cewa an hukunta jarumar akan haka.

Kowa da irin abinda ke fada akan haka, kadanne daga ciki ke goyon bayan jarumar dukda tayi fostin irin wadannan hotunan lokuta dayawa a baya amma baa samu matsala kamar haka ba.

Hoton da ya jawa Rahama shiga cikin halin da take ciki

Amma maganar da ake ciki yanzu shine, yansanda basu gazgata karar da akewa Rahama ba domin babu wani bangare a kurani da littattafai da suka bada damar yanke mata hukunci ba.

A jiya ne ne dai wani daga cikin yan uwan Rahaman wato Usman sadau ya wallafa a shafinsa na facebook cewa

“An gano wanda yai wa Rahama batanci akan hoto kuma bama Musulmi bane, Wani kirista ne da wasu daga cikin yan Kannywood suka hada baki dashi domin bata mata suna”.

“Ya kuma yi nuni da jamaa suyi hakuri daf ake da gano karshen matsalar”.

Ya kara da cewa

Daman “yan kannywood din sun dade suna so su kirkiri wani abu da ze bata wa Rahama suna tinda dadewa amma Allah be basu dama ba”.

Daga karshe yayi addua sannan yace “Allah na nan kuma BaYa bacci, Si ze nuna gaskiya.

  Wole Soyinka Told Buhari That He Can't Defeat Boko Haram by Sitting in Aso Rock