Kannywood: Jerin hotunan da shagulgulan bikin Nuhu Abdullahi

Kannywood Jarumin masana'antar Kannywoood Nuhu Abdullahi, ya angwance da zukekiyar amaryarsa a ranar juma'a wato jiya kenan.

Kannywood Jarumin masana’antar Kannywoood Nuhu Abdullahi, ya angwance da zukekiyar amaryarsa a ranar juma’a wato jiya kenan.

Advertisements
Advertisements

Jarumin ya wallafa kyawawan hotunansa da sabuwar amaryarsa a shafinsa na Instagram

Ya kara da wallafa hotunan wurin daurin aure tare da abokai, ‘yan uwa da abokan sana’arsa Fitaccen jarumin masana’antar fina-finan hausa, Nuhu Abdullahi, ya angwance da kyakyawar amaryarsa Siyama.

An daura auren kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a ranar Juma’a, 4 ga watan Disamban 2020.

Kafin ranar aduarin auren, an fara ganin hotunan jarumin tare da kyakyawar amaryarsa na kafin aure suna yawo a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram.

Hotunan ranar daurin auren jarumi Nuhu Abdullahi da zukekiyar amaryarsa.

Related Post

Jaruman masana’antar tare da masoyan jarumin sun dinga masa kyawawan addu’o’i tare da fatan alheri.

A ranar Alhamis sai ga hotunan shagalin kamun auren da aka yi tare da kyakyawar amaryarsa.

Bayan daurin auren da aka yi a masallacin Juma’a na Alfurqan da ke Alu Avenue a GRA Nasarawa da ke jihar Kano, an ga hotunan jarumin da ‘yan uwa tare da abokan arziki.

Ya wallafa hotunan a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani na Instagram inda aka ga jarumi Ibrahim Maishunku tare da Malam Aminu Saira a wurin daurin aure.