KADPOLY: Wani lecturer ya harbe matarsa sannan ya kashe kansa

Wani tsohon malami da ya koyar a KADPOLY, mai suna Austin Umera ya shayar da mutane mamaki a kan abinda ya aikata.

Advertisements
Advertisements

Ana zarginsa da laifin harbin matarsa, Dokta Maurin, wacce ita ma malama ce a jami’ar jihar Kaduna (KASU), inda daga bisani ya harbe kansa kuam ya fadi ya mutu.

Al’amarin ya faru ne a gidansu da ke layin Kigo a cikin garin Kaduna.

Yanzu haka Dokta Maurin tana kwance a asibitin sojoji na 44 da ke cikin Kaduna, inda ake cigaba da kulawa da lafiyarta.

An adana gawar mijinta a ma’adanar gawa dake asibitin kwararru na Barau Dikko dake garin Kaduna.

Majiyarmu ta samu labarin wannan mummuna al’amarin ne da misalin karfe 10 na daren Laraba.

  Jami'o'i: Gwamnatin tarayya tayi zamanta na karshe da ASSU

Har ila yau, babu cikakke kuma gamsasshen bayani a kan silar aukuwa lamarin amma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige ya tabbatar da aukuwar lamarin.