IBB yayi Kakkausan Zance Kicin Fushi Akan Alakanta Lalacewar Kasannan da Sojoji

IBB, tsohon shugaban kasa na zamanin mulkin soja a Najeriya ya yi martani a kan wadanda ke cewa sojoji ne suka janyo matsaloli a kasar

Advertisements
Advertisements

Babangida ya ce rashin tunani ne ma ace wai sojoji ne suka janyo matsalolin da ke adabar Naejeriya

Tsohon shugaban ya ce tunda farko farar hula ne suka samar da tsarin yadda za a tafiyar da kasar saboda haka hadin gwiwa ne tsakanin farar hula da soja

Tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya ce rashin tunani ne zai sa ace shugabanin mulkin soja ne sanadin matsalolin da ke adabar Najeriya.

Tsohon shugaban sojan, mai shekaru 79 ya bayyana hakan ne a cikin sabuwar hirar da ya yi da Channels TV.

  Boko Haram: Babban rashi a gidan Sojin Najeriya na Kanal D.C. Bako

Babangida wanda ya yi mulkin Najeriya daga 1985 zuwa 1993 ya ce ba za a iya dora wa sojoji alhakin wanzar da matsalolin da ke adabar kasar ba domin farar hula ne suka tsara yadda suke son gudanar da harkokin kasar.

Tsohon shugaban ya ce:

“Ba mu kirkiri matsaloli ba.

Munyi kokarin kafa turbar yadda sauran gwamnatoci za su ginu a kai.

Mafi yawancin ayyukan da aka gudanar har a lokacin demokradiyya, muna da hannu a ciki.

Munyi kokarin dako abinda duniya ke yi a wancan lokacin mun kawo kasar mu.

“Ina ganin sakarci ne a ce mu muka kirkiri matsalolin.

Hadin gwiwa ne tsakanin sojoji da farar hula.

Ku kuka nuna mana yadda abubuwa ke aiki, hukumomin mulki da gwamnatin, dukkansu hakki ne na farar hula.”

Babangida ya ce baya tsamanin za a iya sake yin juyin mulki a Najeriya.

  Kasar Saudiyya Tace Duk Wanda Zaiyi Aikin Hajjin Bana Sai Yayi Allurar Covid-19

“Duk soja mai hankali ba zai so ya jefa kasar cikin matsaloli da takunkumi ba.

Da zarar ka kwace gwamnati, kungiyoyin Afrika da na kasashen waje za su saka ka a gaba.

Ba za a amince da duk wani cigaba da za ka kawo ba. Ba zaka iya aiki kai kadai ba,” inji shi.

A wani rahoton daban, wata kotu da ke Malmo a kasar Sweden ta yanke hukuncin cewa musulmi suna da ikon su rika tafiya suyi salla a lokacin da suke wurin aiki.

Hukuncin ya ce dole masu kamfanoni su rika barin ma’aikatansu Musulmi su rika yin sallolinsu biyar a lokacin da suke wurin aiki.

  Boko Haram: Sun kai mummunan hari a Borno