Rundunar tsaro ta sojojin Najeriya da ke Abuja ta ce ta samu nasarar ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su a yankin arewa maso yammacin ƙasar cikin kwana huɗu.
Advertisements
Advertisements
Rundunar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet, inda ta ƙara da cewa dakarunta na rundunar Sahel Sanity sun kashe tare da kama wasu ‘yan fashin daji.

An ceto mutanen ne a dazuka daban-daban na JIhar Katsina yayin hare-haren da take kaiwa a yankin daga ranar Litinin, 24 zuwa 28 ga watan Agusta.
You must log in to post a comment.